17 GA SATUMBA, 2020
AMIRKA
Wuta Ta Ci Gaba da Yin Barna a Yammacin Amirka
Inda ya faru
Kalifoniya da Oregon da kuma Washington
Bala’i
Wutar daji da take kona wurare da wuri ta kona wurin da fi hekita miliyan biyu (eka miliyan biyar) daga Kalifoniya zuwa Washington
Wutar ta ci gaba da haifar da gurbatacciyar iska
Daya daga cikin wutar ne mafi girma a duk tarihin Kalifoniya
Yadda ya shafi ’yan’uwanmu
Masu shela 4,546 sun gudu sun bar yankinsu
Abubuwan da aka yi hasararsu
Wutar ta halaka gidaje 61
Gidaje 16 kuma sun lalace
Agaji
Kwamitin Aikin Agaji, tare da masu kula da da’ira, da dattawan da suke yankin, sun ci gaba da taimaka wa ’yan’uwan da suke gudu daga yankunan. Suna hakan ba tare da sun karya ka’idodin da aka kafa don cutar Koronabairas ba
Masu shela da bala’in ya shafa sun ga yadda Jehobah ya taimaka musu ta wurin kungiyarsa. Wata ’yar’uwa da wutar ta halaka gidanta ta ce ’yan’uwanmu “suna shirye su yi mana tanadin abin da muke bukata tun kafin mu san cewa muna bukatar abin.”
Ko da yake ’yan’uwanmu maza da mata suna kan fuskantar matsaloli har yanzu, sun ci gaba da ganin yadda Jehobah yake nuna musu jin kai da kuma tausayi.—Yakub 5:11.