1 GA SATUMBA, 2020
AMIRKA
Wutar Daji Ta Yi Barna Sosai a Yammacin Amirka
Inda ya faru
Arewacin Kalifoniya da kuma Oregon
Bala’i
Walkiyar da aka yi wajen sau 14,000 da kuma wasu abubuwa ne suka jawo tashiwar wutar dajin. An sami barkewar wutar daji dabam-dabam fiye da 700 da ta hallaka fadin kasa fiye da eka miliyan daya a arewacin Kalifoniya da wasu wurare a Oregon
Hayaki da toka sun gurbata iskar da ke yankin sosai. A ranar 21 ga Agusta, an sami labari cewa arewacin Kalifoniya ne ke da iska mafi muni a duk duniya
An kuma ba da rahoto cewa a duk tarihin Kalifoniya, biyu daga cikin wutar dajin da suke kan ci har yanzu ne wuta na biyu da kuma na uku mafi girma da aka taba yi
Yadda ya shafi ’yan’uwanmu
Masu shela 936 ne suka gudu daga yankin
Abubuwan da aka yi hasararsu
Gidajen masu shela 2 sun hallaka
Agaji
Wani Kwamitin Aikin Agaji, da masu kula da da’ira da dattawan da suke yankin suna aiki tukuru don su taimaka wa wadanda bala’in ya shafa
’Yan’uwanmu suna godiya sosai don taimakon da suke samu daga kungiyar Jehobah. Wani dan’uwa ya ce: “Ko da me ya faru, ’yan’uwa suna a shirye su zo nan da nan don su taimaka maka. Dukanmu ’yan iyali daya ne.” Kokarin da ake yi don a agaza wa ’yan’uwanmu da bala’i ya fado musu ya tabbatar mana cewa ba abin da ya isa ya “raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana.”—Romawa 8:39.