Koma ka ga abin da ke ciki

15 GA MAYU, 2018
AMIRKA

A Sanadiyyar Duwatsu da Ke Yi Aman Wuta a Hawaii an Umurci Mutane Su Kaura

A Sanadiyyar Duwatsu da Ke Yi Aman Wuta a Hawaii an Umurci Mutane Su Kaura

Tun daga ranar 3 ga Mayu, 2018, dutsen Kilauea ya soma aman wuta a tsibirin Big Island da ke Hawaii a Amirka. Hakan ya sa an ce mutane wajen 2,000 su kaura kuma aman wutar ta halaka gine-gine akalla 36.

A cikin mutanen da aka umurta su kaura har da iyalai guda hudu da Shaidun Jehobah ne da kuma wata ’yar’uwa tsohuwa. Ko da yake babu wani Majami’ar Mulkin da aman wutar ta lalata, girgizar kasa da aka yi a ranar 4 da Mayu ta dan lalata wani Majami’ar Mulki.

Kwamitin Aikin Agaji da kuma ’yan’uwan suna taimaka wa masu shela da bala’in nan ya shafa. Bayan kome ya lafa kwamitin aikin agaji zai bincika don sanin wasu hanyoyin da za a ba da agaji.

Za mu ci gaba da yi wa ’yan’uwanmu da bala’in nan ya shafa addu’a, muna da tabbaci cewa Jehobah za ci gaba da zama wurin buya a lokacin wahala.—Nahum 1:7.