Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA YUNI, 2016
AMIRKA

Shaidun Jehobah Sun Sayar da Wasu Manyan Ofisoshinsu a Brooklyn

Shaidun Jehobah Sun Sayar da Wasu Manyan Ofisoshinsu a Brooklyn

Yadda ginin Towers Hotel yake a zamanin dā.

NEW YORK​—⁠A ranar 24 ga Mayu, 2016, Shaidun Jehobah sun ce suna so su sayar da wani babban gidan bene mai hawa 16 da ke unguwar Clark na 21 a Brooklyn Heights Historic District. A dā, wannan ginin masauki ne da ke da girman kafa 313,768 kuma yana da manyan dakuna a ciki. Shekaru da yawa mutane a fadin duniya sun san da wannan gidan da ke Brooklyn sosai.

A dā, ana kiran wannan ginin Leverich Towers Hotel kuma an soma amfani da shi a shekara ta 1928. Wadanda suka zana wannan ginin su ne Starrett & Van Vleck kuma su ne suka zana wani kamfani mai suna New York City flagship stores of Lord & Taylor and Saks Fifth Avenue. Bayan wasu shekaru, sai wani ya sayi ginin kuma aka canja sunan ginin zuwa Towers Hotel. Gidan yana da babban dakin cin abinci da zaure, kuma za a iya ganin Lower Manhattan da New York Harbor da kuma Brooklyn Bridge daga cikin zauren. Ana kiran wannan ginin “The Aristocrat of Brooklyn Hotels.”

An yi amfani da bishiyar madaci wajen yin matakalar ginin kuma da akwai manyan ginshikai masu kyau sosai.

Duk da cewa ginin ya yi suna da farko amma daga shekara ta 1970, farashin ganin ya fadi. A ranar 14 ga Janairu 1975 ne Shaidun Jehobah suka sayi ginin. A shekara ta 1978, Shaidun Jehobah sun mai da ginin wurin da ‘yan’uwa guda 1,000 da suke aiki a hedkwatarsu za su rika kwana da kuma cin abinci. Wani kakakin Shaidun Jehobah mai suna Richard Devine ya ce: “Mun samun ci gaba sosai a aikin buga littattafai da muke yi. Wannan Ginin yana da isashen wurin da za mu yi amfani da shi wajen kula da ‘yan’uwan da suke zuwa aiki.”

Idan mutane suka hau zuwa zauren Ginin, za su iya ganin hedkwatarmu da Brooklyn da kuma gadan Manhattan da Empire State Building.

A shekara ta 1995, sai Shaidun Jehobah suka soma gyara wannan babban ginin musamman ma dakunan kwana. Malam Devine ya ce: “Mun gama gyara dakunan da kuma canja famfo da kuma wuta a shekara ta 1990. Kari ga haka, mun saka wani matakala mai kyau sosai a babban dakin kuma zai kai har zuwa wurin cin abinci.”

Wani kakakin Shaidun Jehobah mai suna David A. Semonian da yake hedkwatarmu ya ce: “Idan ka fito yawo a hanyar Brooklyn Heights, za ka yi mamakin ganin yadda gidajen suke da kyau. Amma ban da gyarar da muka yi wa ginin, membobin hedkwatarmu sun yi shekaru da yawa suna jin dadin wajen sosai.”

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, 1-718-560-5000