Koma ka ga abin da ke ciki

26 GA FABRAIRU, 2018
AMIRKA

Karin Bayani a Kan Aikin Ba da Agajin da Aka Yi a Lokacin Mahaukaciyar Guguwar Harvey

Karin Bayani a Kan Aikin Ba da Agajin da Aka Yi a Lokacin Mahaukaciyar Guguwar Harvey

Mazaunan jihar Texas a kasar Amirka sun ci gaba da farfadowa daga banar da Mahauciyar Guguwar Harvey ta yi, wanda ta kai kusa da birnin Corpus Christi a ranar 25 ga Agusta, 2017. Kwamiti guda biyu na ja-gorantar ba da agaji don taimaka wa ’yan’uwa maza da mata da bala’in ya shafa.

Wani dan’uwa yana neman Shaidun Jehobah a wurin ba da agaji a birnin Houston da ke Texas.

’Yan’uwa fiye da 7,000 ne suka ba da kansu don su taimaka da share-share wanda ya hada da share gidaje 2,300 na ’yan’uwa. Kimanin ’yan’uwa 1000 ne ke taimaka wa wajen gyare-gyare da gine-gine a kowane mako. ’Yan’uwan sun kammala gyare Majami’u Mulki akalla guda 48, kuma ana kokarin gyara gidaje fiye da 545 a nan gaba. An kiyasta kashe dalla miliyan 8.5 don ba da agaji a wannan wurin, kuma ana sa rai cewa za a kammala aikin a ranar 30 ga Yuni, 2018.

Tun karshen Agusta 2017, wakilai 22 ne daga ofishinmu tare da membobin 7 na Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a kasar suka kai ziyara inda wannan bala’i ya auku don karfafa ’yan’uwan da bala’in ya shafa. Muna addu’a cewa Allah ya ‘karfafa hannuwan’ dukan wadanda suka ba da kai don wannan aikin agaji.—Nehimiya 6:9.

Wanda ke aikin ba da agaji a birnin Aransas Pass da ke Texas.

Media Contacts:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000