20 GA SATUMBA, 2018
AMIRKA
Mahaukaciyar Guguwar Florence Ta Yi Barna A Kudu Maso Gabashin Amirka
Mahaukaciyar Guguwar Florence ta jawo ambaliya da ta yi barna a yawancin wurare a Arewancin Carolina da Kudanci Carolina da wasu jihohi. Guguwar ta hallaka akalla mutane 32 kuma dubbai sun rasa masuguninsu.
Ofishinmu da ke Amirka ta ruwaito cewa ba Mashaidin da ya rasa rai ko ya ji mummunar rauni, duk da haka Shaidu fiye da 4000 sun rasa masuguninsu. Ko da yake abubuwa sun soma gyaruwa, amma akwai wasu wurare da ruwan ambaliya ya hana shiga. Kididdiga ya nuna cewa ambaliyar ruwa ya lalatar da gidaje 351 na ’yan’uwanmu maza da mata da Majami’un Mulki 21.
Kwamitin ba da Agaji sun dauki nauyin raba abinci da ruwan sha da magunguna da kuma wurin kwana. Kari ga haka, aikin ya kunshi cire itatuwan da suka fadi da rukunin masu ba da agaji suke yi. Da yake ambaliyar ta yi barna sosai, ’yan’uwa da ke kusa da kuma wadanda ke nesa sun ba da kansu domin su taimaka kuma Kwamitin ba da Agaji ne ke yi musu ja-goranci. Dattawa da masu kula da da’ira na ziyarta wadanda ambaliyar ta shafa don su karfafa su.
Muna yi wa yan’uwanmu wadanda wannan bala’i ya shafa addu’a kuma muna dokin ganin lokacin da ‘ba za mu ji tsoro ba.’—Isha. 12:2.