Koma ka ga abin da ke ciki

22 GA MAYU, 2017
AMIRKA

Mutane da Yawa Suna Son Zuwa Sabuwar Hedkwatar Shaidun Jehobah

Mutane da Yawa Suna Son Zuwa Sabuwar Hedkwatar Shaidun Jehobah

NEW YORK​—A ranar Asabar, 29 ga Afrilu, 2017, Shaidun Jehobah sun yi wani bikin na musamman don bude gida na biyu a sabuwar ginin Hedkwatarsu a Warwick, New York, kuma mutanen da suka halarci wannan bikin sun fi na farko yawa.

Baki 468 ne suka halarci bikin a ranar Asabar, wato an sami karin kashi 18 bisa dari fiye da Asabar da ta shige. Troy Snyder wanda shi ne manaja na wannan ginin Hedkwatar ya ce: “Mun yi farin cikin ganin makwabtanmu da yawa musamman ma ma’aikatan gwamnati sun zuwa don su zagaya su ga ginin hedkwatarmu. Wadansu makwabtan ma, zuwan su na biyu ke nan domin sun ji dadin abin da suka gani da kuma shaida a lokacin na farko da suka ziyarci wurin nan makon da ya shige.”

Bikin bude gida na biyu ke nan da aka yi kowace asabar tsakanin karfe 10:00 na safe da kuma 4:00 na yamma kuma mutane 863 ne suka zuwa. Mallam Snyder ya ce: “Mun ga nasarar wannan bikin. Wadanda suka halarta sun yaba mana don abubuwan da suka gani a wurin. Muna sa ran sāke marabtar makwabtanmu a duk lokacin da suke so su ziyarce mu domin yawon bude ido da kuma sun so su ga wurin da muke adana kayayyakin tarihi.”

Ingrid Magar

Wata mai suna Ingrid Magar da ke zama a kauyen Tuxedo Park a jihar New York, tana daya daga cikin makwabta da suka zo bikin. Ta taba aiki a kamfani da ke amfani da ginin a dā da ake kira International Nickel Company (wato kamfanin bincike da kuma samun ilimin sanin karafuna) ta yi aiki da kamfanin na tsawon shekara 18 kafin su bar wurin. Ta tuna yadda wurin yake a dā, ta ce: “Na yi farin cikin ganin yadda aka mayar da wannan wurin. Tun da dadewa an yi banza da wannan wurin, babu wanda yake kula da wurin kuma hakan ya sa mutane ba su san abin da zai faru da wurin ba. Duk da cewa wurin ne mai kyau, kun sake inganta wurin sosai.” Kari ga haka, Malama Magar ta yaba wa wadanda suka sayi wurin, ta ce: “Ina ganin ku (wato Shaidun Jehobah) makwabta ne nagari. Kuna da tausayi, kuna kula da mutane, kuna kula da mahalli kuma kuna son mutane. A ganina babban gata ne mu zama makwabtanku.

William Hoppe

Wani mai suna William Hoppe da injiniya ne, da ke bincika ingancin aikin gine-gine a garin Warwick ya bincika ginin hedkwata da Shaidun suka yi a karshen shekaru biyu na kammala ginin kuma ya ce: “Babu shakka Shaidun mutane ne da ke son aikinsu ya yi kyau sosai, kuma ana ganin hakan a yadda aikinsu ke fita tsaf.  . . . Sun burge ni kware da gaske don yadda suka mayar da hankali ga yadda za a tsara mahalli a lokacin da ake aikin ginin da kuma yadda za a kiyaye ta, hakan ya nuna cewa lallai suna son mahallin ya kasance yadda ya kamata. Kuma wannan misali ne mai kyau da ya kamata duk masu aikin gini su bi.”

In da Ake samo Labarin:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000