Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA SATUMBA, 2017
AMIRKA

Shaidun Jehobah sun sayar da gidajensu guda biyu da ke Brooklyn

Shaidun Jehobah sun sayar da gidajensu guda biyu da ke Brooklyn

A ranar 31 ga Agusta, 2017, Shaidun Jehobah sun sayar da gininsu da ke 97 Columbia Heights a Amirka. Gini ne mai fadin kafa 88,610, kuma Shaidu da suke hidima a hedkwatarmu sun yi amfani da wannan ginin a matsayin wurin kwana fiye da shekara talatin. A dā, wani sanannen hotal da ake kira Hotel Margaret ne ke wurin, kuma ana ganin kogin East River da kuma birnin Manhattan. Kari ga haka, yana cikin sanannun gine-gine a unguwar Brooklyn Heights da sukek da rufin masu kyau da kuma wurin da mutane za su iya shakatawa. Kafin wannan lokacin, a ranar 11 ga Agusta, 2017, Shaidun sun kuma sayar da wani gidan kwana da ke 119 Columbia Heights.

A yanzu, sabon hedkwatar Shaidun Jehobah yana garin Warwick da ke jihar New York.

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000