6 GA MAYU, 2016
AMIRKA
Shaidun Jehobah Sun Sayar da Ginin da Suka Fi Dadewa a Ciki da Ke Brooklyn Heights
NEW YORK—A ranar Talata, 26 ga Afrilu, 2016, Shaidun Jehobah sun sayar da ginin da ke 124 Columbia Heights a Brooklyn, a birnin New York. Wannan ginin ya kai wajen eka hudu (ko fegi 25,000), yana da alamar hasumiya a samansa a arewacin yankin Brooklyn Heights Promenade. A watan Disamba 2015 ne ginin ya fito a cikin jerin gidajen da ake so a sayar, an sayar wa wani da bai taba sayen gini a wurin Shaidun Jehobah ba, bayan da mutane da yawa suka taya ginin.
Asali dai, ginin 124 Columbia Heights gidan bene ne mai hawa uku da Henry Ward Beecher, wani sanannen faston Plymouth Church ya zauna a ciki daga shekara ta 1856 zuwa 1881. Jaridar The New York Times ta yi magana a kan muhimmancin tarihin wannan ginin. Jaridar ta ce “wannan ginin ne Mr. Beecher yake zama a lokacin da Shugaban Kasar Amurka Lincoln ya ziyarce shi, kafin shugaban ya sa hannu a takardar ’yantar da bayin da ke kasar da ake kira Emancipation Proclamation.” A watan Mayu 1909 ne Shaidun Jehobah suka sayi ginin, daga baya kuma suka sayi gine-ginen da ke kewaye da wurin, suka mai da shi gidan bene mai hawa 10.
Kakakin Shaidun Jehobah mai suna Richard Devine ya ce: “Muna daukan 124 Columbia Heights a matsayin daya daga cikin gine-ginen tarihi da kungiyarmu ta mallaka. Tun daga shekara ta 1909 ne wadanda suke hidima a hedkwatar Shaidun Jehobah suka soma zama a ginin kuma nan ne gidan rediyonmu yake. Daga shekara ta 1929 zuwa shekara ta 1957 mun yada jawaban da aka dauko daga Littafi Mai Tsarki da makamancin haka a wannan gidan rediyon. A cikin wannan tsawon lokacin, shekaru hudu ne kawai ba mu yi amfani da wannan gidan rediyon wajen yada jawabai ba.”
Shaidun Jehobah sun yi fiye da shekaru 100 a yankin Brooklyn Heights yanzu, amma asali an kafa hedkwatar Watch Tower Bible and Tract Society a Allegheny ne (yanzu yana karkashin birnin Pittsburgh) a jihar Pennsylvania a wajen shekara ta 1884. Wani kakakin Shaidun Jehobah mai suna David Semonian ya ce: “Yadda muka kaura zuwa birnin Brooklyn a shekara ta 1909 ya taimaka wa Shaidun Jehobah su fadada aikinsu na wa’azi a kasashe dabam-dabam a fadin duniya domin birnin yana da tashar jirgin ruwa.”
Sayar da ginin 124 Columbia Heights yana daya daga cikin matakai na baya-bayan nan da Shaidun Jehobah suka dauka wajen karfafa shirin da suke yi na kaurar da hedkwatarsu zuwa Warwick, a birnin New York wanda fadinsa ya kai kusan eka 50. An kusa gama ginin wannan sabon hedkwatar. Mr. Semonian ya dada da cewa: “Abin da muke so mu yi yanzu shi ne mu kaura zuwa sabon gininmu da ke Warwick a arewacin birnin New York. Mun zauna a Brooklyn fiye da shekara dari, amma yanzu Warwick zai zama sabon gidanmu a tarihin kungiyarmu.”
Media Contact:
David A. Semonian, Office of Public Information, tel. +1 718 560 5000