29 GA WATAN AGUSTA, 2017
ANGOLA
An Kai Wa Shaidu da Suke Taron Yanki a Ƙasar Angola Hari da Iskar Gas Mai Guba
A ranar Juma’a da safe, 25 ga watan Agusta, 2017, a taron yanki da aka gudanar a Majami’ar Taron Viana na Shaidun Jehobah a Luanda da ke ƙasar Angola, an kai wa masu halartan taron hari da gas mai guba kuma hakan ya sumar da mutane guda 405 da ke cikin Majami’ar har da wuraren bayan gida da wanka. Muna godiya cewa gas ɗin bai da ƙarfin kashe mutum. An kai waɗanda aka yi wa ɓarnan asibiti kuma yawancinsu sun samu sauki kuma aka sallame su bayan ’yan sa’o’i kaɗan. Hukumomi suna bincike a kan abun da ya faru. An kama maza uku kuma aka kai su tashar ’yan sanda ranar juma’a da rana.
Ofishinmu da ke Luanda ta ba da rahoto cewa waɗanda abin ya shafa suna samun sauki. Sun ce waɗanda suke taron ba su firgita ba kuma sun taimaka ma waɗanda suka ji rauni. ’Yan sanda da ke yankin sun ba da shawara cewa a dakatar da sashen rana na taron. An sake komawa taron yankin ranar Asabar, 26 ga watan Agusta da kuma Lahadi 27. Mutane fiye da 12,000 ne suka halarci taron kuma mutane 188 suke yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah.
Media Contacts:
International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000
Angola: Todd Peckham, +244-923-166-760