9 GA SATUMBA, 2020
ARGENTINA
Fursunoni Suna Nazarin Littafi Mai Tsarki a Wannan Lokacin Annoba
A yankin San Luis da ke kasar Argentina, ’yan’uwanmu suna yin taro kowane mako da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da fursunoni a wani kurkuku mafi tsaro. Suna hakan ta wajen kiransu ta hanyar bidiyo. Wannan ne karo na farko da ake wa’azi a kurkuku ta wannan hanyar a Argentina.
Kafin wannan lokacin, ’yan’uwanmu sun yi shekaru suna zuwa kurkukun nan a kai a kai don su yi taro da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da fursunoni. Amma an dakatar da wannan shirin tun daga lokacin da gwamnatin kasar ta kafa dokar hana fita a watan Maris, 2020. Da yardan hukumar kurkukun, ’yan’uwanmu sun ci gaba da gudanar da taro da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki a kurkukun ta hanyar bidiyo.
Da darektan kurkukun ya ga yadda wannan ziyarar take gyara rayuwar fursunonin, sai shi da matarsa suka soma halartan taron. Ga abin da ya ce: “Yanzu da ba a barin mutane su kawo ziyara a kurkukun, wadannan tarurrukan suna taimaka wa fursunoni su kusaci Allah kuma su sami kwanciyar hankali. Kari ga haka, muna farin cikin ganin yadda wadannan tarurrukan suna taimaka wa fursunonin su yi zaman lafiya da juna. Babu shakka, koya wa fursunoni abin da ke Littafi Mai Tsarki yana taimakonmu mu cim ma burinmu na sa fursunoni su gyara halinsu don su zama mutanen kirki.”
Wani fursuna ya rubuta wasika ga ’yan’uwan da suke shirya wannan ziyarar. A cikin wasikar, ya ce: “A duk ranar da na fita na je taro, nakan mance da matsalolina, da damuwar da ke zuciyata, da bakin ciki da kuma kadaicin da nake fama da shi don an tsare ni. Ina farin ciki kwarai kuma na gode muku sosai.”
Yayin da annobar Koronabairas tana ci gaba da addabar mutane, muna farin ciki cewa ’yan’uwanmu suna taimaka wa mutane su amfana daga sakon da ke Littafi Mai Tsarki.—Ishaya 48:17, 18.