20 GA DISAMBA, 2019
ARGENTINA
Taron Kasashe na 2019 a Buenos Aires, Ajantina
Kwanan Wata: 13-15 ga Disamba, 2019
Wurin Taro: Estadio Único de La Plata, Buenos Aires, Ajantina
Yaruka da Aka Yi Taron: Yaren Kurame na Amirka, Turanci, Sifanisanci
Adadin Mahalarta: 47,555
Wadanda Aka Yi wa Baftisma: 563
Mutane Daga Wasu Kasashe: 6,300
Kasashensu: Bolivia, Amirka ta Tsakiya, Turai na Tsakiya, Chile, Czech-Slovak, Finland, Italiya, Koriya, Paraguay, Peru, Romaniya, Scandinavia, Sifen, Amirka.
Labarai: Maria Anapios, manajar cinikayya na Panamericano Hotel inda mahalarta suka sauka ta ce: “A wannan lokaci da akwai sabani tsakanin kabilu da kasashe da kuma duniya baki daya, ganin irin wannan taron yana da muhimmanci sosai domin misali ne na ’yan’uwantaka da salama da kuma kauna da muke bukata sosai.
ʼYan’uwa suna marabtar baki a tashar jirgin sama
ʼYan jarida suna ganawa da ʼyan’uwa hudu kafin a soma taron
ʼYan’uwa maza da mata suna zuwa wurin taron
Mahallara suna tafi bayan an kammala wani jawabi
An yi wa sababbi baftisma a tafki da ke wurin taron
Dan’uwa Kenneth Cook, memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu yana yin jawabi na karshe a ranar Lahadi
Wasu ’yan’uwa mata suna daukan hoto kuma suna rike da haruffan nan “LOVE,” wato kauna
Mahallara suna daukan hoto
’Yan’uwan da ke hidima ta cikakken lokaci da suka halarci taron suna gai da ’yan’uwa sa’ad da aka tashi taron a ranar Lahadi
’Yan’uwan da ke yanki suna yi wa ’yan’uwan da suka halarci taron wasannin a liyafar da yamma