13 GA DISAMBA, 2019
AUSTRALIYA
Gobara Ta Yi Barna a Ostareliya
Wani dan’uwa da matarsa sun rasa gidansu sanaddiyar gobarar da ta kona daji mai fadin eka miliyan biyu da dubu dari biyar a kudancin New South Wales da Queensland a Ostareliya. Babu wani dan’uwa da ya rasa ransa ko kuma ya ji rauni a gobarar. Kuma babu wani Majami’ar Mulki ko Majami’ar Manyan Taro da ya kone.
Hukuma tana ganin cewa mutane ne suka ta da gobarar. Tun watan Satumba, gobarar ta kashe mutane 6, kuma ta kona akalla gidaje 650.
Kusan ʼyan’uwa 200 ne suka tare daga gidajensu, amma yanzu sun riga sun koma gidajensu. ʼYan’uwa suna kula da ma’auratan da gidansu ya kone, kuma dattawan ikilisiya suna karfafa ʼyan’uwan da gobarar ta shafa.—Ayyukan Manzanni 20:28.