Koma ka ga abin da ke ciki

10 GA JANAIRU, 2020
AUSTRALIYA

Gobarar Daji ta Ki Cinyewa a Ostareliya

Gobarar Daji ta Ki Cinyewa a Ostareliya

Gobarar daji a Ostareliya ta ci gaba da bazuwa don wannan ne shekara mafi zafi a kasar. Tun watan Satumba 2019, an yi munanan gobarar daji a kowace jiha a kasar Ostareliya kuma akwai sauran gobarar daji da ke tafe. A jihar Victoria da New South Wales ne gobarar ta fi tsanani.

Babu wani cikin dan’uwanmu da ya ji rauni ko ya rasa ransa, amma da yawa cikinsu sun yi hasarar dukiyoyinsu, har da gidaje tara da suka kone kurmus. ʼYan’uwa wajen 700 sun tāre daga gidajensu. ʼYan’uwa da yawa sun bar yankin saboda hayakin da ke tashi. Masana sun ce hayakin ya gurbata iska kuma yana da hadari sosai. Yawancin ʼyan’uwa da suka kaura daga gidajensu sun sauka a gidajen danginsu ko abokansu ko kuma masu shela da ke yankunan da gobarar ba za ta shafa ba.

Reshen ofishinmu da ke Australasia ya kafa Kwamitin Agaji guda biyu don su karfafa ʼyan’uwanmu kuma su ba su abin biyan bukata. Masu kula da da’ira biyu da kuma Kwamitin da ke kula da Ofishinmu suna karfafa ʼyan’uwanmu da ke yankunan. Yawancin ʼyan’uwan da ke yankunan da ake gobarar sun gaji sosai. Amma duk da haka, sun ce suna matukar godiya don kaunar da ʼyan’uwanmu suke nunawa.​—⁠1 Bit. 2:⁠17.