29 GA NUWAMBA, 2019
AUSTRALIYA
Melbourne, Ostareliya—2019 “Kauna Ba Ta Karewa”! Taron Kasashe
Kwanan Wata: 22-24 ga Nuwamba, 2019
Wurin Taro: Marvel Stadium a Melbourne, Ostareliya
Yaruka da Aka Yi Taron: Yaren Kurame na Ostareliya, Chinese Cantonese, Chinese Mandarin, Turanci, Koriya, Sifanisanci, Tagalog, Vietnamese
Adadin Mahalarta: 46,582
Wadanda Aka Yi wa Baftisma: 407
Mutane Daga Wasu Kasashe: 6,083
Kasashensu: Ajantina, Kanada, Hong Kong, Indiya, Italiya, Jafan, Koriya, Filifin, Solomon Islands, Afrika ta Kudu, Taiwan, Amirka
Labarai: Manajan Ballarat Wildlife Park ya ce: “Na yi shekara 15 ina aiki a wannan gidan ajiye dabbobin daji, amma a gaskiya, kungiyarku ne na fi jin dadi yin ma’amala da su, su ne kuma rukunin da aka fi tsara da kyau. Ina matukar godiya ga dukanku da kuma wadanda suka kawo ku yawan bude ido.”
Wani manajan otel ya yi kalami game da mutane 340 da suka sauka a otel dinsu, ya ce: “Kowa ya ba da hadin kai don magance matsaloli da suka taso. A gare ni, suna kamar wani babban iyali kuma kowa yana wa juna magana da kuma tallafa wa juna. A gaskiya, na ji dadin yin cudanya da dukansu. Na yi shekara 11 ina aiki a nan, amma wannan rukunin ne kadai ya yi fice.” Don wannan cudanya da ya yi da Shaidun Jehobah, manajar ya halarci taron a ranar Asabar.
’Yan’uwa sun marabci wadanda suka halarci taron sa’ad da suka zo yawon bude ido a ofishinmu da ke birnin Denham Court, a Ostareliya
’Yan’uwa sun shiga filin wasa
Mahalartar taron suna rera wakar yabo ga Jehobah
Wata matashiya ta rungumi mahaifiyarta bayan ta yi baftisma
Dan’uwa David Splane, memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu yana yin jawabi na karshe a ranar Jumma’a
Wadanda suke hidima ta cikakken lokaci suna gai da jama’a
Wadanda suka halarci taro suna daukan hoto
Rukunin ’yan’uwa mata suna wa wadanda suka halarci taron rawa da yamma