Koma ka ga abin da ke ciki

6 GA AFRILU, 2017
AUSTRALIYA

Mahaukaciyar Guguwar Debbie ta Addabi Ostareliya

Mahaukaciyar Guguwar Debbie ta Addabi Ostareliya

An yi wata mahaukaciyar guguwa da aka kira Tropical Cyclone Debbie wadda iskar ke gudun kilomita 260 cikin sa’a guda a yankunan da ke bakin teku da ke arewacin Queensland a ranar Talata, 28 ga Maris, 2017. Wannan guguwar ta kayar da bishiyoyi, ta lalatar da gidaje kuma ta kwashe jiragen ruwa ta jefar da su a bakin teku. Kari ga haka, Guguwar Debbie ta jawo ambaliyar ruwa a birane da garuruwa da yawa a kudancin Queensland da kuma arewacin New South Wales, kuma hakan ya sa duban mutane a wuraren sun rasa wutar lantarki.

Rahotonai da aka samo da farko sun ce babu wani Mashaidin da ya rasa ransa ko ya ji wani mummunar rauni. Amma guguwar ta lalata gidajen Shaidun Jehobah da yawa kuma ta halaka wani gida gaba daya. Kari ga haka, guguwar ta lalata Majami’un Mulki guda biyu.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke Ostareliya ya kafa kwamitocin tara kayan agaji guda biyu don su kai kayan agaji kamar su janareto da abinci da kuma ruwan sha a wuraren da bala’in ya shafa. Dattawa suna taimaka da kuma karfafa ’yan’uwansu da bala’in ya shafa.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana tanadar da kayan agaji ta wajen amfani da gudummawar da ake bayarwa don tallafa wa hidimar Shaidun Jehobah a fadin duniya.

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Australasia: Rodney Spinks, +61-2-9829-5600