Koma ka ga abin da ke ciki

10 GA DISAMBA, 2019
BRAZIL

Kamfen na Musamman a Karkarar Brazil

Kamfen na Musamman a Karkarar Brazil

Dubban Shaidun Jehobah suna iya kokarinsu don su yi wa mutanen da ke zama a yankunan karkara a Brazil wa’azi. An soma wannan kamfen yin wa’azi na musamman a ranar 1 ga Satumba, 2018, kuma an ci gaba da yin sa har ranar 31 ga Disamba, 2019. Har wa yau, Shaidu fiye da 80,000 ne sun saka hannu a wannan kamfen kuma sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane fiye da 16,000.

Brazil ita ce kasa na biyar mafi girma a duniya. An kimanta cewa mutane miliyan 28 ne ke zama a yankunan karkara. Kari ga haka, mutane miliyan 22 ne ke zama a karkara da kauyuka. Wannan kamfen na musamman ya kai yankuna fiye da 1,600. Wasu masu shela sun yi tafiya fiye da kilomita 2,000 don su sami mutane.

Sa’ad da wani mai shela ya je wani gida, ya hadu da wani tsoho da ke surfe kofi da ya girbe daga gonarsa. Mutumin ya gayyace dan’uwan ya shigo, kuma ya kira matarsa ya gaya mata cewa: “Ya zo ya yi mana wa’azi. Mu saurare shi!”

Mutumin da matarsa suka soma yi wa mai shelar tambayoyi. Sun tambaye shi: “Mene ne yanayin matattu? Me ya sa Allah ya kyale mutane suna shan wahala? Ya dace ne su rika biyan zakka? Da yadda za su iya magance matsalar iyali da dai sauransu. Sun ji dadin amsar da mai shelar ya ba da daga Littafi Mai Tsarki, sai mutumin ya bayyana cewa ya yi addu’a da safiyar kuma ya roki Allah ya ba shi amsar wadannan tambayoyin. Iyalin sun halarci taronsu na farko da yamma a ranar, kuma sun ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki.

Sa’ad da Shaidu suke wa’azi gida-gida a wani wuri, sai aka soma ruwan sama mai karfi, kuma suka shiga wani asibiti don su nemi mafaka. Sa’ad da suke wurin, sun tambayi wata mata da ’yarta irin tambayoyin da za su so su yi wa Allah. Yarinyar ta ce za ta so ta ga kakarta da ta rasu. Shaidun suka karanta masu nassosi da suka yi magana game da tashin matattu suka kuma nuna masu bidiyo mai jigo The Resurrection​—Soon a Reality.

Da shaidu suka ziyarci matan a gidan ta, sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita da iyalinta. Matan da yaranta yammata sun halarci taro a wani birni da ke kusa da su kuma sun ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki ta hanyar waya.

Littafi mai tsaki ya annabta cewa za a samu mazauna a mulkin Allah zuwa “iyakar duniya.” Wannan kamfen na musamman a yankunan karkara a Brazil ya nuna cewa Jehobah yana dokin cika wannan annabcin.​—Zabura 71:8.