Koma ka ga abin da ke ciki

2 GA FABRIRU, 2017
CHILE

An Yi Wata Gobara A Chile

An Yi Wata Gobara A Chile

Shaidun Jehobah suna taimaka wa ‘yan’uwansu da kuma wasu mutanen da gidajensu suka kone sanaddiyar gobarar da aka yi, wannan gobarar ta halaka babban wuri sosai a tsakiyar Chile da kuma kuduncinta. Hukumomi sun ce ba a taba yin irin wannan bala’in gobarar ba domin wutar ta yi sati biyu tana ci ba fashi.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke Chile sun ce ba wani cikin Shaidun Jehobah da ya ji wani rauni ko kuma rasa ransa a sakamakon gobarar. Wasu suna bukatar su gudu su bar gidajensu amma kuma wasu shaidun sun ba su masauki.

Kari ga haka, gobarar ta kone gidaje biyar na Shaidun Jehobah. Ofishin Shaidun Jehobah da ke kasar sun kafa wani kwamitin tara kayan agaji don su taimaka da kai kayan agaji.

Hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah suna amfani da gudummawar da ake bayarwa wajen tanadar da kayan agaji daga hedkwatarsu.

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Chile: Jason Reed, +56-2-2428-2600