8 GA JANAIRU, 2021
CROATIA
Girgizar Kasa Ta Yi Barna a Kasar Kuroshiya
Inda ya faru
Kusa da garin Petrinja, garin da ke da nisan kilomita 50 kudu da Zagreb, babban birnin Kuroshiya
Bala’i
A ranar 29 ga Disamba, 2020, an yi girgizar kasa mai karfin maki 6.4 a kasar Kuroshiya. Wannan ita ce girgizar kasa mafi karfi da aka taba yi a kasar
Yadda ya shafi ’yan’uwanmu
Babu ko daya daga cikin ’yan’uwa 91 a yankin da ya ji rauni
’Yan’uwanmu guda 29 sun rasa gidajensu
Abubuwan da aka yi hasararsu
Gidaje guda 9 sun lalace sosai
Gidaje guda 16 sun dan lalace
Majami’ar Mulki da ke Sisak ya dan lalace kadan
Agaji
Ofishinmu da ke kasar Kuroshiya ya kafa Kwamitin Aikin Agaji. Kwamitin yana aiki tare da masu kula da da’ira guda biyu da kuma dattawa a yankin don su tanadar wa ’yan’uwan abubuwa da za su karfafa bangaskiyarsu, da kayan agaji, da kuma wurin kwana ga wadanda suka rasa gidajensu. Kwamitin yana bin ka’idodin kāre kai daga cutar korona yayin da yake aikin
Addu’armu shi ne Jehobah ya ci gaba da ba ma ’yan’uwanmu karfin da suke bukata don su iya jimre wannan mawuyacin lokaci.—1 Bitrus 5:10.