Koma ka ga abin da ke ciki

12 GA NUWAMBA, 2020
FILIFIN

Mahaukaciyar Guguwa Ta Daki Filifins Sau Biyu

Mahaukaciyar Guguwa Ta Daki Filifins Sau Biyu

Inda ya faru

Kudancin Luzon da tsibiran da ke kusa da ita

Bala’i

  • A ranar 25 ga Oktoba, 2020, mahaukaciyar guguwar mai suna Typhoon Molave, da ake kira Quinta a Filifins, ta yi barna sosai a lardin Albay da ke yankin Bicol a Luzon a kasar Filifins. Guguwar ta kuma yi barna sosai a wasu wurare a tsibirin Luzon

  • A ranar 1 ga Nuwamba, 2020, mahaukaciyar guguwar mai suna Super Typhoon Goni, da ake kira Rolly a Filifins, ta daki tsibirin Catanduanes, da ke yankin Bicol da ke Luzon. Wannan mahaukaciyar guguwa mai Mataki na 5 ta ci gaba da yin barna a wasu wurare, har ma da wuraren da Typhoon Molave ta riga ta daka

  • Guguwar nan da ta auku sau biyu, ta sa an yi ruwan sama da iska mai karfin gaske da suka jawo ambaliya da karancin ruwan sha, kuma ta sa an dauke wuta a wurare da yawa. Har yanzu yana da wuya a kira mutanen da ke yankunan nan ta waya ko intane

  • Ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ya kwaso laka daga Tudun Mayon da ta lalata gidaje da yawa kusa da tudun

Yadda ya shafi ’yan’uwanmu

  • Darurruwan ’yan’uwanmu sun gudu sun bar gidajensu

  • Wata ’yar’uwa mai shekara 89 ta dan ji rauni sa’ad da take gudu ta bar gidanta da ya rushe gabaki daya

Abubuwan da aka yi hasararsu

  • Gidaje 134 da Majami’un Mulki guda 8 sun dan lalace

  • Gidaje 75 da Majami’un Mulki guda 8 sun lalace sosai

  • Gidaje 101 da Majami’ar Mulki 1 sun lalace gabaki daya

Agaji

  • Masu kula da da’ira, da dattawan yankunan suna aiki tare da Kwamitin Aikin Agaji guda shida don su tabbata cewa ’yan’uwa sun sami abinci da ruwan sha da wurin kwana da kuma wasu abubuwan da suke bukata. ’Yan’uwanmu suna musu tanadin abubuwan da suke bukata kuma suna karfafa su, ba tare da sun karya ka’idodin da aka kafa don cutar koronabairas ba

Za mu ci gaba da yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu da bala’in nan ya shafa. Mun san cewa Jehobah zai ci gaba da zama “Uba mai yawan tausayi,” da zai ta’azantar da ’yan’uwanmu da suke fama da bala’in nan.​—2 Korintiyawa 1:3.