4 GA SATUMBA, 2017
FINLAND
Shaidun Jehobah Sun Karfafa Mutane Bayan Wata Hari da Aka Kai a Birnin Turku da Ke Kasar Finland
HELSINKI—Rana Juma’a 8 ga Agusta, 2017, an kashe wata ’yar’uwarmu a Findland, kuma bincike ya nuna cewa dan ta’adda ne da ke fakon mata ya kai harin. Ban da ’yar’uwarmu, dan ta’addan ya kashe wata mata ya kuma yi ma wasu mutane takwas rauni a harin da ya kai cikin kasuwa a birnin Turku da ke yankunan kudu maso yammacin kasar Finland. Ba dadewa ba bayan harin, wakilai daga ofishin Shaidun Jehobah na Finland da masu kula da da’ira da kuma dattawa sun karfafa wadanda bala’in ta shafa.
Kakakin Shaidun Jehobah a Finland mai suna Veikko Leinonen, ya ce: “Wannan bala’i ne mai muni sosai. Muna bakin ciki sosai don wata ’yar’uwarmu da majagaba ce ta rasa ranta a wannan harin yayin da take wa’azi a inda jama’a suke. Mun san cewa, duk da kiyayewa, ba ya kasancewa da sauki a wasu lokuta a iya guje wa bala’i kamar ta’addanci. Amma za mu ci gaba da karfafa juna, musamman iyalin ’yar’uwarmu da aka kashe. Muna addu’a cewa Jehobah ya ci gaba da ta’azantar da wadanda bala’in ya shafa. Za mu kuma ci gaba da daukan matakai masu kyau da za su taimaka mana don kada mu rika damuwa yayin da muke ci gaba da yin wa’azi.”—Mai-Wa’azi 9:11; Romawa 15:13; Filibbiyawa 4:6, 7.
Don a karfafa ‘yan’uwa, an tura wasikar karfafa daga ofishinmu da ke Finland ga dukan ikilisiyoyi. ’Yan’uwanmu da ke ofishin da ke kasar sun shirya taro ta musamman domin karfafa ’yan’uwa maza da mata guda 135 da ke taimaka wa a yin wa’azi a wurin da jama’a suke a birni Turku. ’Yan’uwan da ke hidimar majagaba sun nuna gaba gadi kuma suna son su ci gaba da yin wa’azi a inda jama’a suke.
Mutane da yawa da ke zama a Turku sun damu sosai don wannan hari da aka kai. Domin ana yi wa kasar Finland ganin tana daya daga cikin kasashen da mutane suke zama hankali kwance. Ba da dadewa ba bayan harin da aka kai, ’yan’uwanmu sun soma nuna wa mutane sun damu da su yayin da suke wa’azi kofa zuwa kofa har ma da kasuwa don su karfafa mutane.
’Yan’uwan da ke ofishinmu a Finland na godiya sosai ga ’yan’uwa a fadin duniya domin addu’o’insu da saƙonnin da suka tura da kuma taimakonsu. (1 Bitrus 2:17; 5:9) Muna godiya musamman ga Jehobah, “Allah mai ba da jimrewa da ƙarfafawa.”—Romawa 15:5.
Media Contacts:
International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000
Finland: Veikko Leinonen, +358-400-453-020