20 GA NUWAMBA, 2020
LABARAN DUNIYA
Guguwar Eta Ta Yi Barna Sosai a Amirka ta Tsakiya, Tsibiran Cayman, Bahamas, Jameka, Meziko, da Kasar Amirka
Inda ya faru
Amirka ta Tsakiya, Tsibiran Cayman, Bahamas, Jameka, Meziko, da kasar Amirka
Bala’i
Mahaukaciyar guguwa Eta mai mataki 4 ta yi barna sosai a Puerto Cabezas, a kasar Nicaragua, a ranar 3 ga Nuwamba, 2020. Guguwar ta kuma yi barna sosai a wasu wurare a Amirka ta Tsakiya
Abin bakin ciki, wani yaro mai shekara tara, jikan wasu ’yan’uwanmu a jihar Tabasco a Meziko, ya rasu sanadiyyar ambaliyar da guguwar ta jawo
Daga baya, guguwar Eta ta canja salo kuma ta daki tsibirin Grand Cayman, da Bahamas, da Jameka. Guguwar ta kuma isa gefen teku da ke Meziko kuma ta yi barna a wasu wurare a Amirka
Yadda ya shafi ’yan’uwanmu
Costa Rica
Masu shela 108 sun gudu daga gidajensu
Masu shela 7 sun rasa duk abin da suka mallaka
Guatemala
Masu shela 163 ne suka bar gidajensu da farko; daga baya masu shela 85 sun koma gidajensu
Iyalai 3 sun rasa duk abin da suka mallaka
Kari ga haka, ruwa ya tare iyali 1, mai masu shela 3, a gidan sama. Daga baya an kawo musu dauki
Honduras
Masu shela 1,984 ne suka bar gidajensu da farko; amma a kalla guda 376 sun riga sun koma gidajensu
Jameka
Masu shela 4 sun gudu daga gidajensu
Meziko
A jihar Chiapas da Tabasco, an taimaki masu shela 1,618 su gudu daga gidajensu; guda 112 sun riga sun koma gidajensu
Nicaragua
Masu shela 238 ne bala’in ya sa suka gudu daga gidajensu; guda 232 sun riga sun koma gidajensu
Panama
Masu shela 27 ne suka gudu daga gidajensu; guda 6 sun riga sun koma gidajensu
Amirka
Masu shela 48 ne suka gudu daga gidajensu; guda 27 sun riga sun koma gidajensu
Abubuwan da aka yi hasararsu
Bahamas
Gida 1 ya lalace
Costa Rica
Gidaje 3 sun hallaka
Gidaje 6 sun lalace
Guatemala
Kasa ta zaftare ta sauko kan Gidaje 2 kuma ta hallaka su
Honduras
Majami’un Mulki 7 sun dan lalace
Nicaragua
Gidaje 73 sun lalace
Tsibirin Grand Cayman
Gidaje 4 sun lalace
Majami’ar Mulki 1 ta dan lalace
Jameka
Gidaje 50 sun lalace
Majami’ar Mulki 1 ta lalace
Amirka
Gidaje 141 sun lalace
Majami’un Mulki 9 sun dan lalace
Agaji
Ofishinmu a Amirka ta Tsakiya ta riga ta kafa Kwamitin Ba da Agaji guda uku don su kula da aikin ba da agaji ga wadanda bala’in ya shafa. Biyu daga cikinsu suna kasar Meziko, dayan kuma yana Honduras. A sauran kasashen da guguwar ta shafa, Kwamitocin Ba da Agaji da suke agaza wa wadanda annobar koronabairas ta shafa ne suke kula da wadanda guguwar ta shafa
A yankin Ofishinmu da ke Amirka, ikilisiyoyi da Kwamitocin Ba da Agaji da suke agaza wa wadanda annobar koronabairas ta shafa ne suke kula da wadanda guguwar ta shafa
A duk wuraren da guguwar nan ta shafa, Masu kula da da’ira suna karfafa iyalan da bala’in ya shafa
’Yan’uwa maza da mata da suke wuraren da bala’in bai kai ba su ma suna tallafa wa wadanda bala’in ya shafa da wurin kwana da kuma abinci
’Yan’uwanmu suna aikin agajin nan ne ba tare da sun karya ka’idodin da aka kafa don cutar koronabairas ba
Duk da hasarar da guguwar nan ta jawo, muna samun karfafa idan muka ga yadda ’yan’uwanmu suke taimaka wa juna. Muna da tabbaci cewa Jehobah Allahnmu zai ci gaba da zama “wurin buya . . . a lokacin wahala.”—Zabura 9:9.