Koma ka ga abin da ke ciki

13 GA NUWAMBA, 2019
LABARAN DUNIYA

Rahoto na 2019 na Dauke da Adadi Mafi Yawa na Mutane da Suka Yi Baftisma Cikin Shekara 20

Rahoto na 2019 na Dauke da Adadi Mafi Yawa na Mutane da Suka Yi Baftisma Cikin Shekara 20

Muna farin ciki sanar da ku cewa a shekara ta 2019, mutane sama da 300,000 ne suka yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Wannan shi ne karo na farko tun shekara ta 1999 da adadin mutanen da suka yi baftisma ya wuce 300,000. Muna yaba wa Jehobah da ya albarkaci wa’azi da almajirantar da mutane da muke yi da zuciya daya!

Kari ga haka, a shekara ta 2019 an yi wasu abubuwa na musamman, hakan ya kunshi: taron kasashe, an fito da Littafi Mai Tsarki a wasu harsuna. da nuna kauna masu gamsarwa. Ga wasu adadin daga rahotanni na dukan duniya. *

  • Adadin Kasashe Da Suke Ba Da Rahoto: 240

  • Mahalarta Tunawa da Mutuwar Yesu: 20,919,041

  • Adadin Masu Shela: 8,683,117

  • Adadin Wadanda Suka Yi Baftisma: 303,866

Irin wannan rahoto mai gamsarwa na karfafa mu mu bi shawarar Yesu da ke jigon shekara ta 2020: “Ku je, ku sa su zama almajiraina, . . .  kuna yi musu baftisma.”​—Matiyu 28:19.

^ sakin layi na 3 Nan ba da dadewa ba, za a fito da cikakken bayani game da Rahoton Hidima ta Shekarar 2019 a dandalin jw.org.