Koma ka ga abin da ke ciki

8 GA JANAIRU, 2021
LABARAN DUNIYA

Wa’azi na Musamman a 2020: ’Yan’uwa a Fadin Duniya Sun Sami Karfafa Daga ‘Abin da Ba Za Su Taba Mantawa’ Ba

Wa’azi na Musamman a 2020: ’Yan’uwa a Fadin Duniya Sun Sami Karfafa Daga ‘Abin da Ba Za Su Taba Mantawa’ Ba

Shaidun Jehobah za su rika tunawa da watan Nuwamba 2020 a matsayin wata mai muhimmanci a tarihinsu. Annoba ta tilasta wa yawancin mutane zama a gida. Mun daina yin wa’azi ta hanyoyin da muka saba yi na dan lokaci. Duk da haka, Shaidun Jehobah sun yi shela game da Mulkin Allah a fadin duniya ta wajen yin wa’azi na musamman. A duk fadin duniya, miliyoyin masu shela sun yi aiki tukuru don su tura Hasumiyar Tsaro ta 2, 2020 zuwa ga ’yan kasuwa da jami’an gwamnati da malamai da abokansu da danginsu da kuma jama’a gabaki daya. Wadanda suka saurari wa’azin sun koyi abubuwa da yawa. Amma wadanda suka yi wannan aiki ma sun yi farin ciki kuma sun sami karfafa.

Ga wasu labarai da ’yan’uwanmu a fadin duniya suka bayar:

AUSTRALASIA

’Yar’uwa Lucinda Furkin

Wata ’yar’uwa mai shekara goma sha takwas mai suna Lucinda Furkin, da ba ta dade da yin baftisma ba kuma tana zama a kasar Ostareliya ta rubuto cewa: “Ko da yake na yi fama da rashin lafiya mai tsanani a lokacin da ake wa’azin, na ga cewa Jehobah yana karfafa ni, kamar dai yana rike da hannuna ne yana ba ni karfin jimrewa.”

Wani mahaifi a Niyu Zilan ya bayyana yadda wa’azin ya taimaka wa iyalinsa. Ya ce: “Muna da yara mata hudu masu shekaru 7 da 9 da 11 da kuma 13. Mun gaya wa kanmu cewa wannan wa’azi na musamman aiki ne da Ubanmu Jehobah ya ba mu mu yi. Hakan ya taimaka wa iyalinmu mu iya yin wa’azi kowace rana a lokacin wa’azi na musamman din.”

BOTSWANA

Wani mai kula da da’ira mai suna Kagiso Marumo da matarsa Lydia sun tura wannan mujallar ta na’ura ga danginsu da ba Shaidu ba. Danginsu sun gode musu sosai. Wata danginsu da likita ce ta gaya musu cewa sun tura mata mujallar a lokacin da ya dace. Ta bayyana cewa wasu da take musu jinya suna da tambayoyi game da Allah da Littafi Mai Tsarki, yaranta kuma sun shiga kungiyar asiri. Dan’uwa Marumo da matarsa sun kira wannan danginsu kuma suka fara yin nazari da ita da yamman. Yanzu suna nazari tare sau biyu a mako.

Dan’uwa Kagiso Marumo da matarsa, Lydia

KANADA

’Yar’uwa Soroya Thompson

Wata ’yar’uwa majagaba mai suna Soroya Thompson, da take zama a birnin Ontario ta rubuto cewa: “Shirin ya taimaka mini in mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci kuma ya nuna min cewa akwai aiki sosai da ya rage mu yi. Kari ga haka, ya tuna mini cewa Jehobah yana kaunar mu kuma ba ya so kowa ya hallaka. Hakan ya sa na dada kwazo yayin da muke wa’azin.”

Wata ’yar’uwa daga yankin British Columbia ta ce: “A wannan mawuyacin lokaci da muke ciki, na yanke shawarar yin hidimar majagaba na dan lokaci don in daina damuwa da kuma bakin ciki. Ya taimaka mini in daina bakin ciki kuma iyalina ma sun amfana.”

Ofishinmu na Kanada ya ce wannan wa’azi na musamman da aka yi ya taimaka wa iyalai su kusaci juna. Kari ga haka, ya taimaka wa yara su ga cewa suna da amfani a yin wa’azi domin sun rubuta wasiku da kansu, ko sun taimaka wa iyalansu su saka wasiku a cikin ambulan ko su saka tambari a jikin ambulan ko kuma su nemi adireshin mutane.

FINLAND

Wani mai kula da da’ira mai suna Tuomisto da matarsa sun ce: “Watan Nuwamba ne wata mafi duhu a kowace shekara a nan Finland. Don haka, ’yan’uwa da yawa, musamman majagaba sun yi godiya don wannan wa’azi na musamman da ya taimaka musu kada su yi fama da ciwon bakin ciki.”

Dan’uwa Timo Tuomisto da matarsa, Eeva

Bayan wasu ma’aurata sun aika mujallar ga wani mutum da suka waye shi, sai ya tura musu sakon godiya kuma ya ce: “Yau, [na karanta] littafin Yakub. Kuma littafin ya ce bangaskiya wadda ba ta da ayyukan da suke tabbatar da ita banza ce. A koyaushe, Shaidun Jehobah suna zuwa wurin mutane su bayyana musu abin da ke Littafi Mai Tsarki kuma su koyar da su. Suna yin abubuwa da ke karfafa bangaskiyar mutane.”

GIRKA

Ofishinmu na Girka ya ce: “Annobar korona da ka’idodin kāriya da aka kafa sun gajiyar da mutane da yawa. Wannan wa’azi na musamman ya karfafa su. ’Yan’uwa da yawa sun ce hakan ya sa sun wartsake!”

’Yar’uwa Suzie Kontargiri

’Yar’uwa Suzie Kontargiri ta yi hidimar majagaba na dan lokaci duk da cewa tana fama da rashin lafiya kuma mijinta ba Mashaidin Jehobah ba ne. Ta ce: “Wa’azi na musamman din ya taimaka mini in daina bakin ciki. Nakan tashi daga barci da farin ciki, sa’an nan in yi ayyukan gida, in dafa abinci, in kula da mijina, kuma in soma wa’azi. Mijina da ba ya bauta ma Jehobah yakan tambaye ni: ‘Ba za ki yi wa’azi yau ba?’ domin ya saba gani na ina wa’azi da farin ciki tare da ’yan’uwana mata.”

JAFAN

’Yar’uwa Tamaki Hirota ta rubuta wasiku ga hukumomin gwamnati. Ta ce: “Jehobah ne ya fara yin wa’azi ta wasika. Ya rubuta wasiku guda 66 ga ’yan Adam, kuma ’yan Adam sun yi shekaru suna karantawa don su iya kusantar sa. Jehobah ya san cewa wannan hanyar yin wa’azi tana kawo sakamako mai kyau. Ba zan taba mantawa da wannan wa’azi na musamman da muka yi ba.”

’Yar’uwa Tamaki Hirota

SRI LANKA

A cikin kuskure, an gaya wa ’yar’uwa Meharaja Vijaya da ’yar’uwa Imayanathan Amutha cewa su rubuta wasika zuwa ga mutum daya. Mutumin ya wurgar da wasika ta farko ba tare da ya bude ta ba. Sai aka tura masa wasika ta biyu. Da ya gani sai ya gaya wa kansa cewa tun da an tura wasikar har sau biyu, da alama sakon da ke ciki yana da muhimmanci sosai. Ya karanta mujallar kuma ya kira ’yar’uwa da ta aika wasika ta biyun ya gaya mata cewa yana so a yi nazari da shi.

Daga hagu zuwa dama: ’Yar’uwa Meharaja Vijaya da ’Yar’uwa Imayanathan Amutha

Wata jami’ar gwamnati ta kira ofishinmu da ke Sri Lanka bayan ta karanta mujallar. Ta ce ba ta taba haduwa da Shaidun Jehobah ba duk da cewa ita Kirista ce. Bayan ta yaba wa abin da ke mujallar da kuma dandalinmu, sai ta ce: “Ta yaya zan zama Mashaidiyar Jehobah?” Nan da nan ’yan’uwa suka yi shiri don wani ya ziyarce ta.

AMIRKA

Wani mai shela dan shekara 13 wanda ake yawan tattauna siyasa a makarantarsu, ya bayyana yadda yin wa’azi na musamman ya taimaka masa. Ya ce: “Yin wa’azin ya sa na kasance da karfin zuciyar gaya wa malamaina dalilin da ya sa ba na saka baki a harkokin siyasa. Hakan ya dada karfafa bangaskiyata.”

’Yar’uwa Margit Haring

Yadda ’Yar’uwa Margit Haring ma ta ji ke nan. Ta rubuta cewa: “Wa’azi na musamman din ya sa na kara kasancewa da karfin zuciya da kuma kwazo. Da farko, tunanin yadda zan yi wa’azi ga ’yan kasuwa da jami’an gwamnati ya sa ni tsoro. Na koyi yadda zan kāre imanina ba tare da zafin rai ba, kuma na san hakan zai taimaka mini a nan gaba.”

Wani dattijo ya ce: “Abin da ya fi ratsa mini zuciya shi ne yadda ’yan’uwa da yawa suka yi hidimar majagaba duk da cewa suna fama da rashin lafiya mai tsanani. Da sun so, da za su iya cewa ba su da karfi, amma ba su yi hakan ba. Sun yi amfani da damar domin su ma su saka hannu a wa’azi na musamman din. Irin farin cikin da suka yi da kuma yadda suka nuna godiya ga Jehobah da ’yan’uwansu, ya sa dukan mu zub da hawaye.”

Akwai labaran ’yan’uwa da yawa, da abubuwan da suka fada game da wa’azin a fadin duniya, da ba za mu iya ambata su duka a nan ba. Yin wa’azin Mulkin Allah ga miliyoyin mutane ya sa mu farin ciki sosai.—Yohanna 15:11.