Koma ka ga abin da ke ciki

27 GA SATUMBA, 2018
LABARAN DUNIYA

Kotun Sulobakiya ta Wanke Sunan Martin Boor Bayan Shekaru 90 da Aka Saka Shi a Kurkuku

Kotun Sulobakiya ta Wanke Sunan Martin Boor Bayan Shekaru 90 da Aka Saka Shi a Kurkuku

Shekaru 90 da suka shige, an saka dan’uwa Martin Boor a kurkuku domin ya ki shiga soja saboda imaninsa. Amma a ranar 18 ga Satumba, 2015, wata kotu a Sulobakiya ta yanke hukunci cewa bai dace da aka yi hakan ba. Karar Martin Boor ita ce wadda ta fi dadewa da kotu ke yin shari’a a kai da aka canja hukuncin.

An Saka Wani Mutum a Kurkuku Don Ya Nuna Karfin Zuciya

Hoton dan’uwa Martin Boor a lokacin da aka kama shi.

Martin ya zama Mashaidin Jehobah a shekara ta 1920, a lokacin yana dan shekara 17. A watan Oktoba 1924, hukuma ta bukaci ya shiga soja. Amma saboda imaninsa, ya ki shiga soja ko ransuwa cewa zai nuna aminci ga aikin soja. A sakamakon haka, hukuma ta dauka ya sami tabin hankali kuma suka ce likita ya duba lafiyarsa. Likitan ya gano cewa dan’uwa Boor ba shi da tabin hankali, sai likitan ya ce: “Abubuwan da ya yi imanin da su ne suka sa ya ki yin ba don ra’ayin karya ba.”

Da yake dan’uwa Martin yana da cikakkiyar lafiya, a ranar 2 ga Afrilu, 1925, kotu ta yanke hukunci cewa ya yi babban laifi da ya ki shiga soja. Wannan saurayi da ke da aure ya nuna karfin zuciya sa’ad da kotu ta yanke masa hukuncin yin shekaru biyu a kurkuku. Hakan ya hada da yin aiki mai wuya da kuma rashin samun isashen abinci sa’ad da yake kurkukun. Amma Martin bai yi shekaru biyu a kurkuku ba. A ranar 13 ga Agusta, 1926, an sake shi domin ya kasance da halaye masu kyau sa’ad da yake kurkuku.

Hukuncin da Kotun Turai da Ke Kare Hakkin Bil Adama ta Yanke

Dan’uwa Boor ya mutu a ranar 7 ga Janairu, 1985. A shekara ta 2004, iyalinsa sun daukaka kara don a wanke sunan Dan’uwa Boor amma ba su yi nasara ba. Bayan shekara bakwai, sun sake daukaka kara cewa kotun Bratislava na Daya ta sake bincike hukuncin da aka yanke wa dan’uwan. Hakan ya faru ne bayan hukunci da kotun Turai da Ke Kare Hakkin Bil Adama ta yanke a shari’ar Bayatyan v. Armenia, cewa za ta kāre wadanda suka ki shiga soja don imaninsu. Amma abin takaici, ba a yi nasara ba duk da kwakkwarar dalilan da aka ba da na wanke sunan dan’uwa Martin, domin kotu ta ki yanke hukunci na karshe. Sai da aka bincika hukunci da aka yanke ma wani da ya ki shiga soja domin imaninsa ne abubuwa suka soma canjawa.

Hukunci Mai Muhimmanci da Aka Yanke wa Vajda

Kamar dan’uwa Martin Boor, Imrich Vajda ma wani Mashaidin Jehobah ne da ya ki shiga soja. An saka shi a kurkuku a shekara ta 1959 da 1961 a lokacin gwamnatin Kwaminis. A ranar 13 ga Maris, 2014, kotu a Sulobakiya ta yanke hukunci cewa a wanke sunan dan’uwa Imrich Vajda domin bai yi laifi ba, bisa ga dokar Czechoslovak Doka Na 119/1990 Coll. An kafa wannan dokar ne don a taimaka ma wadanda aka nuna musu rashin adalci a lokacin da gwamnatin Kwaminis ke mulki. A shari’ar Imrich Vajda, kotu ta ce Sulobakiya ta bi hukuncin da kotun Turai da Ke Kare Hakkin Bil Adama ta yanke a shari’ar Bayatyan cewa dole ne a yi ma wadanda aka tuhume su da laifi don kin shiga aikin soja ahuwa.

Saboda hukunci mai kyau da aka yanke wa Vajda, iyalin dan’uwa Martin Boor sun daukaka kara zuwa kotun Bratislava na Daya cewa dan’uwa Martin Boor bai yi laifi ba. A ranar 18 ga Satumba, 2015, kotun ta yarda ta sake saurarar karar kuma ta canja hukuncin da aka yanke wa dan’uwan. Bayan shekaru 90 da aka saka dan’uwa Martin Boor a kurkuku da kuma bayan ya yi shekaru 30 da mutuwa, kotu ta wanke sunansa cewa bai yi laifi ba don ya ki shiga soja.

Hukuncin da kotun Turai da Ke Kare Hakkin Bil Adama ta yanke da kuma wanda wasu kotuna suka yanke a shari’a da aka yi wa Vajda sun taimaka wajen magance rashin adalcin da aka yi tun da dadewa. A yanzu, kotunan Sulobakiya sun wanke sunan Shaidun Jehobah guda 51, yawancin su an saka su ne a kurkuku daga shekara ta 1948 zuwa 1989.