Koma ka ga abin da ke ciki

24 GA JANAIRU, 2018
LABARAN DUNIYA

An Nada Dan’uwa Kenneth Cook a matsayin Memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

An Nada Dan’uwa Kenneth Cook a matsayin Memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

A ranar Laraba, 24 ga Janairu, 2018, an sanar wa ’yan’uwan da ke hidima a Bethel a Amirka da Kanada cewa an nada Dan’uwa Kenneth Cook a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Kafin a nada Dan’uwa Cook, yana hidima a matsayin mataimakin Kwamitin Rubuce-Rubuce na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.

Dan’uwa Cook ya soma hidimar majagaba a ranar 1 ga Satumba, 1982, kuma ya soma hidima a hedkwatarmu na Amirka a ranar 12 ga Oktoba, 1984. A yanzu haka, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana da membobi takwas.

Muna addu’a cewa Jehobah ya ci gaba da saka wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da alheri yayin da take kula da ayyukan Shaidun Jehobah a fadin duniya.—1 Tasalonikawa 5:12, 13

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000