16 GA MAYU, 2017
LABARAN DUNIYA
Shaidun Jehobah Sun Soma Taron Yanki
NEW YORK—A ranar 19 ga Mayu 2017 ne Shaidun Jehobah suka soma taronsu na yanki na kwana uku da ke da jigo “Kar Ka Gaji!” Za a yi taron a wurare dabam dabam a fadin duniya har zuwa farkon shekara ta 2018. Kamar yadda suka saba yi, Shaidun suna kan yin kamfen na gayyatar mutane zuwa taron.
Ba a biyan kudi kafin a halarci taron, kuma ba a tara baiko. Wani wakilin Shaidun Jehobah a hedkwatarsu da ke Warwick, New York mai suna David A. Semonian ya ce: “Mutane kusan miliyan goma sha uku ne suka halarci taron yankinmu a shekarar da ta shige. “Muna sa ran ganin mutane fiye da hakan a wannan shekarar.”
An raba taron zuwa sashe 52 kuma za a gudanar da su a hanyoyi dabam-dabam. Hakan ya kunshi gajerun jawabai, ganawa da kuma bidiyoyi. Kari ga haka, za a nuna wani bidiyo mai jigo Ku Tuna da Matar Lutu a kowace rana. Za ku iya ganin ranar da kuma wurin da za a yi kowane taron yankin a dandalin shaidun Jehobah, wato jw.org/ha. ’Yan jaridu za su iya tuhumar ofishin shaidun Jehobah da ke kusa da su don karin bayani, ko kuma idan suna so su yi bidiyon taron.
“Dan’uwa Semonian ya ce: “Abubuwa da yawa a duniya suna iya tayar mana da hankali kuma su sa mu gaji. Amma taronmu na wannan shekarar zai taimaka wa Shaidu da wadanda ba Shaidu ba su ci gaba da jimrewa da kuma yadda za su magance matsalolin rayuwa.”
Media Contact:
David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000