Koma ka ga abin da ke ciki

5 GA YUNI, 2018
GUATEMALA

Dutse Ya Yi Aman Wuta a Guatemala

Dutse Ya Yi Aman Wuta a Guatemala

A ranar Lahadi 3 ga Yuni, 2018, dutse da ake kira Fuego ta yi aman wuta da ta kai tsawon kilomita 9 a Guatemala. Da akwai akalla ikilisiyoyi guda goma a yankunan da bala’in ya shafa. Muna farin ciki cewa babu wani daga cikin ’yan’uwanmu da ya ji rauni a sanadiyyar wannan bala’i, amma an kaurar da guda takwas domin kada kome a same su. Kamar yadda littafin 2 Korintiyawa 8:14, 15 ya umurta, masu kula da da’ira da ke kusa da yanki sun tura wa ’yan’uwan abubuwa da suke bukata, sun yi musu tanadin wajen kwanciya da kuma yadda za su rika zuwa inda suke so.