Koma ka ga abin da ke ciki

26 ga Yuni, 2017
GUATEMALA

Mummunar Girgizar Kasa Kusa da Iyakar Meziko da Guatemala

Mummunar Girgizar Kasa Kusa da Iyakar Meziko da Guatemala

Shaidun Jehobah suna taimaka wa mutanen da wata babbar girgizar kasa ta afko masu a yammancin Guatemala kusa da Meziko a ranar Laraba, 14 ga Yuni, 2017. Wani rahoto da aka samo kwanan nan ya ce akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a sakamakon wannan girgizar kasar.

Babu wani cikin Shaidun Jehobah da ya ji wani rauni ko ya rasa ransa a inda aka yi girgizar kasar. Amma akwai majami’un mulki 11 da kuma gidajen shaidun Jehobah 17 da suka lalace. Ofishin reshen Shaidun Jehobah na Amirka ta Tsakiya da ke birnin Meziko ta shirya kwamiti uku a Guatemala don su je su duba yawan abin da ya lalace kuma su hanzarta yadda za a rarraba kayan agaji wa wadanda girgizar ta shafe su.

Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun taimaka wajen inganta shirin da cibiyar rassa ta ya yi na ba da kayan agaji. Sun yi haka ne ta wurin yin amfani da kudaden da aka samo daga gudummawar da ake bayarwa a aikin wa’azi da ake yi a faɗin duniya.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Mexico: Gamaliel Camarillo, +52-555-133-3048

Guatemala: Juan Carlos Rodas, +502-5967-6015