Koma ka ga abin da ke ciki

31 GA OKTOBA, 2019
INDIYA

Shaidun Jehobah Sun Fitar da Littafi Mai Tsarki a Yaren Telugu a Indiya

Shaidun Jehobah Sun Fitar da Littafi Mai Tsarki a Yaren Telugu a Indiya

A ranar 25 ga Oktoba, 2019, Dan’uwa Ashok Patel, memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a Indiya ya fitar da juyin New World Translation of the Holy Scriptures a yaren Telugu a taron yanki da aka yi a wata babban majami’a da ake kira Hyderabad International Convention Centre a birnin Hyderabad da ke Indiya.

A Indiya, an kamanta cewa mutane miliyan 91 da dari tara ne suke yaren Telugu, wannan ya sa ya zama yare na uku da mutane suka fi yi a Indiya bayan Hindi da Bengali. A yanzu akwai masu shela kusan 6,000 da ke wa’azi a yankunan da ake yaren Telugu, amma mutane 8,868 ne suka halarci taron. Wannan ya nuna cewa za a samu karuwa sosai, don a wannan shekara an kafa da’irori biyu a wannan yaren.

Daya daga cikin mafassara da suka yi wannan aiki na shekara biyar ya ce matasa ba sa fahimtar kalmomin da aka yi amfani da su a Littafi Mai Tsarki na yaren Telugu da suke amfani da shi a dā. “Sa’ad da matasa suka karanta wannan sabon juyi na New World Translation, zai zama kamar Jehobah yana musu magana ta yi amfani da kalmomi na zamani da ke da saukin fahimta.” Wani mafassari ya kara da cewa, “Idan muna wa’azi, mutane suna fahimtar abin da muke karantawa nan da nan.”

Bugu da kari, da yake yawancin Littafi Mai Tsarki a yaren Telugu ba su yi amfani da sunan Allah, Jehobah ba, New World Translation zai taimaka wa masu yaren su san sunan Allah Madaukaki. Ban da haka, zai taimaka musu su fahimci ma’anar kalmomin nan kurwa da ruhu, don sauran juyin Littafi Mai Tsarki a yaren Telugu sun fassara wadannan kalmomin bisa abin da mutane suka yi imani da shi a addinin Hindu.

Wani mai shela ya ce, “Ina ganin cewa mutane da za su karanta wannan Littafi Mai Tsarki a yaren Telugu za su ga cewa Jehobah yana kaunar su sosai!” Babu shakka, wannan sabon Littafi Mai Tsarki a yaren Telugu zai taimaka wa masu karatu su ‘dandana su ga Yahweh mai alheri ne.’​—Zabura 34:8.