Koma ka ga abin da ke ciki

23 GA JANAIRU, 2017
ITALIYA

Wata Ambaliyar Kankara Ta Addabi Italiya

Wata Ambaliyar Kankara Ta Addabi Italiya

A ranar Laraba 18 ga Janairu 2017, wata ambaliyar kankara da ake kira avalanche ta addabi garin Abruzzo da ke tsakiyar Italiya. A wannan garin ne aka yi girgizar kasa a watar Agusta shekarar da ta shige kuma ta binne wani babban otel tare da mutane 30 da ke ciki. Bayan wannan bala’in kankarar sai aka yi girgizar kasa mai karfi dabam dabam hudu a wannan ranar. Abin da ya kara sa yanayin muni shi ne ruwan kankarar da aka yi a makon da ya shige kuma hakan ya sa an dauke wutar lantarki a birane da yawa.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke Italiya sun rohoto cewa babu wani cikin Shaidun Jehoba da ya ji wani rauni ko kuma ya rasa ransa. Amma yanzu ofishin suna iya kokarinsu don su tabbatar da cewa sun ji labarin ko wanne iyali cikin Shaidun Jehobah da ke wurin da wannan bala’in ya fi shafa. Dattawan Shaidun Jehobah da ke wajen suna tanadar wa Shaidun abinci da ruwan sha da itacen girki da kuma wasu abubuwan biyan bukata. Ofishin sun ci gaba da taimakawa a inda akwai bukata.

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Italy: Christian Di Blasio, +39-06-872941