Koma ka ga abin da ke ciki

16 GA JANAIRU, 2017
JAMHURIYAR DEMOKIRADIYYAR KWANGO

Shaidun Jehobah Sun Taimaka wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Shafe Su a Kwango

Shaidun Jehobah Sun Taimaka wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Shafe Su a Kwango

Shaidun Jehobah sun ci gaba da taimaka wa ’yan’uwansu da kuma wasu da ambaliyar ruwan da aka yi a Kwango ya shafa, wannan ambaliyar ta auku a garin Boma, da ke da nisan kilomita 470 a kuduncin Kinshasa a makon 26 ga Disamba.

Ambaliyar ta shafi iyalan Shaidun Jehobah 39 kuma daya daga cikin Shaidun ya rasa ransa. Kari ga haka, ambaliyar ta halaka gidajen Shaidun Jehobah biyar gaba daya, gidaje biyar kuma sun dan lalace.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke Kango sun kai abinci da kuma tufafi wa Shaidun da wannan bala’in ya shafa a yammancin kasar. Shaidun Jehobah da ke biranen Matadi da Muanda, sun ba da kansu don su taimaka wa ‘yan’uwansu, tsakaninsu nisan kilomita 80 ne.

Hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah sun yi amfani da gudummawar da ake bayarwa don aikin hidima wajen tanadar da kayan agaji zuwa Kwango daga hedkwatarsu a Warwick, New York.

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Democratic Republic of the Congo: Robert Elongo, +243-81-555-1000