14 GA SATUMBA, 2018
JAMUS
Bikin Nuni a Kassel a kasar Jamus ta kamala taron gunduma na cikan shekaru 70.
A watan Yuli 1948, a garin Kassel a kasar Jamus, Shaidun Jehobah sun yi taro da ya zama mafi girma na Shaidu a Turai bayan Yaki Duniya na Biyu. Shaidun sun yi bikin nuni a Kassel don cika shekaru 70 na tunawa da wannan taron na farkon da suka yi. Kuma mutane fiye da 2000 ne suka halarci wannan taron da aka yi na kwanaki 12. Gidajen telibijin da na Jaridun Jamus ne suka watsa rahotannin wannan taron.
An kafa tarihi a taron gunduma na Kassel inda mutane 23,150 suka halarci taron, kuma mutane 1,200 ne suka yi baftisma. Wani abin lura kuma shi ne yawanci wadanda suka halarci taron da kuma ba da jawaban mutane ne da suka tsira daga kurkukun kisan-gilla da ke wurin a dā. Domin tunawa da hakan, a bikin bude taron, Dr. Gunnar Richter, Darekta na Breitenau Concentration Camp Memorial Site ya ba da jawabi, inda ya bayyana yadda Shaidun Jehobah suka sha wahala a lokacin mulkin ’yan Nazi.
A bikin, an nuna hotuna da suka nuna yadda aka ragargaza Kassel a Yakin Duniya na Biyu. A lokacin da ’yan’uwan ke shirin wannan taron, hukumomi sun ba su wani fili da ke da ramuka cike da ruwa da bama-bamai suka tona. Kuma sa’ad da Dan’uwa Kurt Rex da ya halarci taron, ya yi bayani a kan yadda suka dauki kusan makonni hudu suna shirya wurin, ya ce: “Aikin na da matukan wuya. Da farko mun yi amfani da bokitai don mu kwashe ruwan da ke ramukan. Sa’an nan muka cika su da duwatsu da kasa na gidajen da aka ragargaza a anguwar. Yin hakan bai zama mana da sauki ba domin ba mu da abubuwan yin irin wannan aikin. Da yake ana yawan ruwan sama, muna yawan jikewa sa’ad da muke aikin.” Duk da haka, ’yan’uwanmu sun tattaro duwatsu da yashi da ya kai kimanin tsawon mita 10,000.
A Jawabin da ya yi, kakakin ofishin Shaidun Jehobah a kasar Jamus mai suna Wolfram Slupina, ya bayana irin halin da ’yan’uwa maza da mata suka nuna a lokacin shirya taron, ya ce: “Da aka sake su daga kurkuku, ba su mai da hankali ga rashin adalcin da aka yi musu ba ko kuma su soma tunanin daukar fansa ba. . . . Amma sun kasance da karfin gwiwar ci gaba da aikinsu.”
A jawabinta ga wadanda suka halarci taron, kansilar garin da ta zo a madadin mahukunta a yankin Kassel, mai suna Esther Kalveram ta ce: “Wannan taron ba abu mai muhimminci ba ne kawai ga Shaidun Jehobah amma har da garin Kassel gabaki daya.”
Taron gunduma na 1948 da kuma bikin cika shekaru 70 da aka yi a 2018, ya ba da shaidar yadda mutanen Jehobah suka kuduri niyyar ci gaba da taruwa domin samu ilimin Littafi Mai Tsarki duk da kalubalen da suke fuskanta.—Zabura 35:18.