Koma ka ga abin da ke ciki

26 GA YUNI, 2018
KAMARU

Ana Kan Gina Sabon Ofishi a Kasar Kamaru

Ana Kan Gina Sabon Ofishi a Kasar Kamaru

Wajen mutane hamsin ne a iyalin Bethel a birnin Douala a Kamaru. Nan ba da dadewa ba, za su kaura daga ofishinmu da ke Bonaberi zuwa sabon ofishin da ake ginawa a Logbessou. Wannan sabon gini alama ce na yadda ake samun ci gaba a Kamaru. A shekara ta 2017 mutane fiye da 100,000 ne suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu, wannan adadin ya ninka yawan Shaidun Jehobah a kasar sau biyu.

Yan’uwa suna saka abin da zai kāre ginin daga tsawa.

Wurin da ake gina ofishin yana kusa da Majami’ar Babban taro. An soma aikin ne da tona tushen ginin. Idan aka kammala wannan aikin, tsarin ginin zai kasance ne kamar sauran gine-gine da suke yankin. Za a yi ginin ofisoshi dabam, kamar yadda aka nuna a hoto. Ana sa rai cewa za a kammala aikin nan ba da dadewa ba kuma iyalin Bethel za su iya kaura zuwa sabon ofishin a karshen shekara ta 2019.

Gilles Mba wanda ke aiki a sashen ba da rahoto a Bethel a Kamaru, ya ce: “ ’Yan’uwanmu da suka ba da kansu don wannan aikin, sun nuna irin halin Ishaya.” (Ishaya 6:8) Ya kara da cewa: “Yadda ’yan’uwan suke yin wannan aikin, yana karfafa dukanmu a iyalin Bethel kuma ya sa mu kara kwazo a aikinmu. Muna marmarin ganin mun kammala wannan gini don amfani da shi Kamar yadda ya kamata wato don daukaka sunan Jehobah.”

Wasu daga cikin ’yan’uwa fiye da 2,800 da suka halarci taron na musamman don su san yadda za su tallafa a aikin ginin ofishinmu.