Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA NUWAMBA, 2019
MEZIKO

An Fitar da New World Translation a Yaren Maya

An Fitar da New World Translation a Yaren Maya

Ranar 25 ga Oktoba 2019, rana ce mai muhimmanci ga ’yan’uwanmu 6,500 da ke yaren Maya. A ranar ce aka fitar da juyin New World Translation a yaren Maya. Dan’uwa Esteban Bunn memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a Amirka ta Tsakiya ne ya fitar da juyin Littafi Mai Tsarki a taron yanki da aka yi a birnin Mérida, da ke jihar Yucatán, a kasar Meziko. An yi taron a Majami’ar Babban Taron da ke Mérida kuma wasu sun kalli taron ta hanyar bidiyo a wani babban wurin taro da ke birnin Poliforum Zamná. Wannan Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa ’yan’uwanmu sosai a wa’azi domin akalla mutane 762,000 ne suke yaren Maya a kasar Meziko da Amirka.

A dā, juyin New World Translation of the Christian Greek Scriptures (littafin Matiyu zuwa Ru’ya ta Yohanna) ne kadai ake da shi a yaren Maya. An fitar da wannan juyin a ranar 14 ga Disamba, 2012, kuma tun lokacin an buga kusan guda 29,000.

Wani mafassari ya ce: “Mutane masu yaren Maya suna son Baibul kuma suna daukaka shi sosai. Amma mutane da yawa ba sa fahimtar abin da suka karanta a yarensu. Saboda haka, mun fi mai da hankali ga yin amfani da kalmomi masu saukin ganewa da mutanen ke amfani da su kullum.”

A yankin, akwai bambance-bambance a yadda ake yaren. Saboda haka, wani kalubale da mafassaran suka fuskanta shi ne yin fassara don kowa ya fahimta. Shi ya sa aka fassara jigon Baibul din da sauki zuwa Biblia ich maya, wato “Baibul a Yaren Maya.” Kari ga haka, da akwai karin bayani fiye da 6,000 a cikin Baibul din. An yi amfani da wannan karin bayani don a ba da ma’anar wasu kalmomi don masu karatu su fahimci wasu ayoyin da suke karantawa.

Babu shakka, wannan sabon juyin abinci ne “a kan lokaci,” kuma zai taimaka wa ’yan’uwa da ke yaren Maya sosai sa’ad da suke nazari da kuma wa’azi.​—Matiyu 24: 45.