Koma ka ga abin da ke ciki

31 GA OKTOBA, 2019
MEZIKO

An Fitar da New World Translation a Yaren Tzotzil

An Fitar da New World Translation a Yaren Tzotzil

A ranar 25 ga Oktoba, 2019 a taron yanki da aka yi a jihar Chiapas, a kasar Meziko, a filin wasan Poliforum na Tuxtla Gutiérrez. Dan’uwa Armando Ochoa, memban Kwamiti da Ke Kula da Ofishinmu a Amirka ta Tsakiya ya fitar da juyin New World Translation a yaren Tzotzil. ’Yan’uwa sun kalli taron ta hanyar bidiyo a wani babban wurin taro. Mutane 3,747 ne suka halarci taron.

An fitar da New World Translation of the Christian Greek Scriptures (littafin Matiyu zuwa Ru’ya ta Yohanna) a yaren Tzotzil a ranar 26 ga Disamba, 2014. An raba wa mutane da ke yaren Tzotzil, wadanda suke zama a tuddan jihar Chiapas na kasar Meziko da kuma kewayen jihar. Daga cikin mutane fiye da 16,000,000 ’yan asalin Meziko, mutane wajen 500,000 ne suke yaren Tzotzil, hakan ya hada da Shaidun Jehobah 2,814.

Mafassara a yaren Tzotzil sun fuskanci kalubale da yawa. Alal misali, littattafan da aka wallafa a yaren Tzotzil ba su da yawa kuma kamus kadan ne suke da shi. Kari ga haka, da akwai yankuna bakwai da yarensu ya dan bambanta. Saboda haka, mafassaran suna bukatar su zabi kalmomin da dukan masu yaren Tzotzil za su fahimta.

Daya cikin mafassaran ya ce: “Domin wannan juyin ya yi amfani da sunan Allah, Jehobah, hakan zai taimaka wa masu karatu su kulla dangantaka na kud da kud da shi. Juyin Littafi Mai Tsarki guda biyu da aka wallafa a yaren Tzotzil sun yi amfani da sunan Allah sau daya kawai a karin bayani a littafin Fitowa. Wannan shi ne juyin Baibul na farko a yaren Tzotzil da ya mayar da sunan Allah a dukan inda ya kamata ya kasance.”

Kari ga haka, wani mai shela dan Tzotzil ya ce “sauran juyin Baibul a yaren Tzotzil suna da tsada sosai. Mutane kalilan ne suke iya sayen su. Amma wannan sabon Baibul kyauta ne ake rarraba shi.”

Babu shakka, wannan sabon Baibul zai amfani dukan masu yaren Tzotzil da “suka san cewa suna bukatar kulla dangantaka da Allah.”​—Matiyu 5:​3, New World Translation.