Koma ka ga abin da ke ciki

20 GA SATUMBA, 2017
MEZIKO

Girgizar Kasa ta Auku a Tsakiyar Kasar Meziko

Girgizar Kasa ta Auku a Tsakiyar Kasar Meziko

A ranar 19 ga Satumba 2017, girgizar kasa mai karfin awo 7 da digo 1 ta afka wa tsakiyar kasar Meziko, mutane fiye da 200 ne suka rasa rayukansu. An sami rahoto daga ofishinmu da ke Amurka ta tsakiya game da bala’in.

Abin takaici an ba da rahoto cewa wata ’yar’uwa ta rasa ranta a birnin Meziko a sanadiyyar girgizar kasar. Ban da haka ma, ba a san inda wata ’yar’uwa take ba, bayan da gidanta ya rushe a girgizar kasar. A birnin Puebla, wata ’yar’uwa ta ji rauni sosai, a birnin Meziko kuma wata ‘yar’uwa tana kwance a asibiti sanadiyyar raunuka da ta ji.

Saboda bala’in an kaurar da ’yan’uwan da ke ofishinmu da ke kasar na dan lokaci, amma sun koma bayan kome ya lafa. Babu wanda ya ji rauni a ofishin kuma babu abin da ya sami ginin.

Za mu ci gaba da yi wa ’yan’uwanmu da ke kasar addu’a domin wannan mummunar yanayi da suka sami kansu a ciki. Mun san cewa Jehobah zai ci gaba da taimaka musu don ya san irin “damuwar” da suke ciki.​—Zabura 31:7.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Mexico: Gamaliel Camarillo, +52-555-133-3048