Koma ka ga abin da ke ciki

12 GA SATUMBA, 2017
MEZIKO

Mahaukaciyar Gugugwar Lidia ta Auku a Meziko

Mahaukaciyar Gugugwar Lidia ta Auku a Meziko

A ranar 1 ga Satumba, 2017, mahaukaciyar guguwar Lidia ta auku a yankin ruwa da ke tsakanin Meziko da California. Ko da yake karfin guguwar ya ragu sosai a ranar Asabar, amma guguwar ta jawo ruwan sama mai karfi da ba a taba yi ba tun shekara ta 1933. Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu sanadiyyar guguwar.

An sami rahoto daga ofishin Shaidu Jehobah da ke birnin Meziko cewa, ambaliyar ta kwashe wata Mashaidiya yayin da ke kokarin zuwa gida kuma hakan ya sa ta rasa ranta. Amma an ceci wasu ‘yan’uwa guda uku da ambaliyar ta kusan kwashe su. Kari ga haka, guguwar ta yi kacakaca da gidaje guda takwas. Duka mutanen da bala’in ya shafa ‘yan’uwansu ko kuma Shaidun Jehobah da ke wurin ne suke kula da su.

A hedkwatarmu, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suna tanadin kayan agaji ta wajen amfani da gudummawa da aka bayar don wa’azi a fadin duniya.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Mexico: Gamaliel Camarillo, +52-555-133-3048