15 GA NUWAMBA, 2019
NEPAL
An Saki Shaidun Jehobah Biyu Daga Kurkuku a Nepal, Suna Jiran Shari’a
A ranar 4 ga Nuwamba, 2019, bisa wasu sharuda an saki ’yan’uwa mata biyu masu suna Tirtha Maya Ghale da Pushpa Ghimire daga kurkuku, bayan sun yi wata daya daga cikin watanni uku da kotu ta yanke za su yi. An tsare su don bin imaninsu duk da cewa dokar kasar Nepal da na kasashen duniya ta ba mutane ’yancin bin addininsu.
A watan Nuwamba, 2018, an kama ’yan’uwa Ghale da Ghimire don suna wa’azi a kan titi. Bayan sun yi kwanaki 13 a kurkuku, sai aka biya kusan dalla 930 don a yi belinsu, wannan kudi ne mai yawa sosai. Amma hukumomin sun ci gaba da bincike.
A ranar 10 ga Disamba, 2018 ne aka fara yi musu shari’a a kotu, kuma an yi watanni goma ana shari’a. A ranar 2 ga Satumba, 2019, kotu da ke yankin Rupandehi ta yanke wa ’yan’uwa mata biyu hukuncin yin watanni uku a kurkuku, kuma su biya akalla dalla 23.
Alkalin ya tuhumi ’yan’uwan da laifin yin kokarin sa mutane su canja addininsu da kuma rarraba littattafan addini. Kasar Nepal tana cikin Majalisar Dinkin Duniya kuma ta sa hannu a Kungiyar Kāre ’Yancin ’Yan Adam. Saboda haka, ya wajaba gwamnati ta tabbatar da cewa ’yan kasar sun sami ’yancin zabar canja addininsu kuma su sanar da hakan a fili ko kuma a boye.’Yan’uwa Ghale da Ghimire ba sa tilasta wa mutane su canja addini, amma suna rarraba littattafan addini ga wadanda suke so su saurara. Lauyoyin da ke wakiltan ’yan’uwan sun daukaka kara zuwa Koton Koli a ranar 31 ga Oktoba, 2019. Kotun ta yanke hukuncin cewa bai kamata a tsare ’yan’uwan sa’ad da ake jira a yi shari’a ba. Don haka, ta ba da umurni sake su yayin da suke jira kotun ta yanke hukunci na karshe.
Muna addu’a Jehobah ya ci gaba da ba wa ’yan’uwa Ghale da Ghimire ruhunsa, kuma ya karfafa su, ya sa su rika farin ciki kuma su kasance da kwanciyar hankali yayin da suke jiran sakamakon daukaka kara da suka yi.—Romawa 15:13.