Koma ka ga abin da ke ciki

27 GA DISAMBA, 2019
NIJERIYA

An Fitar da Juyin New World Translation a Yaren Tiv

An Fitar da Juyin New World Translation a Yaren Tiv

A ranar 20 ga Disamba, 2019, Dan’uwa Wilfred Simmons, memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a Nijeriya ya fitar da juyin New World Translation of the Christian Greek Scriptures (littafin Matiyu zuwa Ru’ya ta Yohanna) a yaren Tiv. Ya yi sanarwar a taron yanki na “Kauna Ba Ta Karewa” da aka yi a City Bay Event Center a birnin Makurdi da ke jihar Benue a Nijeriya.

An fitar da wannan juyin Littafi Mai Tsarki da ya dauki shekara biyu kafin a gama fassarawa a lokacin da ya dace. Yaren Tiv yana cikin harsuna da aka fi yi a Nijeriya, don masu yin yaren sun fi miliyan biyar. A cikin shekara uku da suka shige, adadin masu shela da ke yaren Tiv ya karu sosai, wato daga 600 zuwa 1,012.

Muna da tabbaci cewa wannan sabon juyi zai sa a sami karuwa sosai a yankuna da ake yaren Tiv, don “sun nuna, sun kuma isa girbi.”​—Yohanna 4:35.