2 GA OKTOBA, 2020
RASHA
Ana So A Yanke wa ’Yan’uwa Maza Hudu da Ma’aurata Daya Hukuncin Yin Shekara Bakwai a Kurkuku a Rasha
Ranar da Za A Yanke Hukuncin
A ranar 5 ga October, 2020, * Kotun Gundumar Zasviyazhsky da ke Birnin Ulyanovsk zai sanar da hukuncin da ya yanke a kan Dan’uwa Aleksandr Ganin, da Khoren Khachikyan, da Andrey Tabakov, da Mikhail Zelenskiy, da Dan’uwa Sergey Mysin da matarsa, Nataliya. Za a iya jefa dukansu a kurkuku kuma watakila su kai shekara uku zuwa bakwai a wurin, bisa ga hukuncin da za a yanke wa kowannensu. Wanda ya shigar da karar yana so kotu ya kwace kudadensu da motocinsu da suka kai kimanin dala 20,000 (wajen naira 7,650,000).
Karin Bayani
Aleksandr Ganin
Shekarar Haihuwa: 1957 (Ekhabi, Tsibirin Sakhalin)
Tarihi: Ya yi fiye da shekara 20 da yin baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah. Yanzu ya yi ritaya daga aikin da yake yi kuma yana son yin aikin lambu
Khoren Khachikyan
Shekarar Haihuwa: 1985 (Yerevan, Armenia)
Tarihi: Yana da digiri a fannin ilimin tattalin arziki. Ya yi gasar dambe sa’ad da yake matashi. Shi mutumin kirki ne da kuma saukin kai
Ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah don ya so ya san Allah sosai kuma ya bi dokokinsa. Yadda aka tsara Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa abin da ke ciki gaskiya ne, kuma ba ya saba wa abin da ya fada. Wani abin da ya burge shi ke nan
Sergey Mysin
Shekarar Haihuwa: 1965 (Kulebaki, Yankin Nizhny Novgorod)
Tarihi: Yayin da yake karatu ya zama injiniya ne ya hadu da matarsa Nataliya. Sun yi aure a 1991. Suna da yara biyu da suka yi girma, kuma sun yi fiye da shekara 20 suna bauta wa Jehobah tare. Yana son yin wasanni, musamman wani irin wasan kwallo da ake kira lacrosse
Nataliya Mysina
Shekarar Haihuwa: 1971 (Leningrad, wato inda ake kira Saint Petersburg a yau)
Tarihi: Iyayenta sojoji ne. Ta taba zama a Jamus kafin ta kammala karatu a jami’a a matsayin likitan magunguna. Tana son yin dahuwa
Andrey Tabakov
Shekarar Haihuwa: 1973 (Minsk, Belarus)
Tarihi: Ya kware wajen aiki da na’urar kwamfuta. A 2006, ya auri matarsa mai suna Marina. Sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma sun yi baftisma. Yana son aiki da na’urori, musamman rediyo da kwamfuta
Mikhail Zelenskiy
Shekarar Haihuwa: 1960 (Bulaesti, Moldova)
Tarihi: Dā ya yi aiki a jirgin ruwa kuma ya taba tukin babban mota. A 1989, ya auri matarsa Victoria. Ba da dadewa ba su biyun suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Hakan ya sa sun kaunaci Jehobah kuma sun yi baftisma
Yadda Labarin Ya Soma
Wajen shekara uku da suka shige, jami’an tsaro a Rasha da ake kira Federal Security Service (FSB) sun soma yin shisshigi a ayyukan da ’yan’uwanmu a Ulyanovsk suke yi. Alal misali, sun soma daukan maganganun da ’yan’uwan suke yi a waya. A ranar 24 ga Fabrairu, 2019, jami’an tsaron sun soma yin bincike a kan Dan’uwa Mysin da matarsa, da Dan’uwa Khachikyan da Tabakov da Zelenskiy da niyyar kama su da laifi.
Kwana uku bayan hakan, jami’an tsaron sun shiga gidajen ’yan’uwan nan wajen karfe 5 na safe, wato Dan’uwa Khachikyan, da Tabakov, da Zelenskiy. Sun kama su ukun kuma suka kai su kurkuku na dan lokaci. A wannan safiyar har ila, wani ya kira ’Yar’uwa Mysina a waya. Mutumin ya ce mata motarta ya sami wata matsala, kuma ya ce ita da maigidanta Sergey su fito waje. Da suka bude kofar gidansu, sai kawai jami’an tsaron FSB suka shiga gidan karfi da yaji. Sun bincika ko’ina kuma suka kwace na’urorinsu. Sai suka kama ma’auratan suka tafi da su.
Washegari, Kotun Gundumar Leninsky da ke Yankin Ulyanovsk ya ba da umurni cewa a kai Dan’uwa Mysin kurkuku kafin a yi masa hukunci. ’Yar’uwa Mysina da sauran ’yan’uwa ukun kuma an tsare su a gida.
Dan’uwa Mysin ya yi kwana 55 a kurkuku yana jiran hukuncin da za a yi masa, kuma ya yi kwana 123 yana tsare a gida. ’Yar’uwa Mysina, da Dan’uwa Khachikyan, da Tabakov, da Zelenskiy kuma, sun yi kwana 50 zuwa 55 suna tsare a gida, bisa ga hukuncin da aka yi wa kowannensu.
A ranar 15 ga Mayu, 2019 da safe, jami’an tsaro sun bincika gidan Dan’uwa Ganin, kuma suka kama shi. Ya yi kwana biyu a wani kurkuku da ake kulle mutane na dan lokaci.
A yanzu, akwai wasu ayyuka da gwamnati ta hana ’yan’uwa shidan nan yi. Amma har ila, hukumomin da ke yankin suna tsananta musu a hanyoyi dabam-dabam. Sun hana Dan’uwa Mysin da matarsa, da Dan’uwa Tabakov cire kudi daga asusun bankinsu. Dan’uwa Mysin da matarsa suna da kusan dala 6,313 (wajen naira 2,417,879) a asusun bankinsu, Dan’uwa Tabakov kuma yana da kusan dala 7,575 (wajen naira 2,901,225) a asusun bankinsa.
Yayin da ake ci gaba da tsananta wa ’yan’uwanmu saboda imaninsu a Rasha, addu’armu ita ce abin da Kalmar Allah ta fada zai ci gaba da ba su kwarin gwiwa, inda ta ce: “Allah shi ne wurin buyanmu da karfinmu, taimakonmu na kurkusa lokacin wahala.”—Zab. 46:1.
[Karin bayanni]
^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar