1 GA FABRAIRU, 2023
RASHA
“Ba Yanayina Ne Kawai Nake Bukata In Canja Ba”
Nan ba dadewa ba, kotun yankin Vladimir na Birnin Kovrovskiy zai sanar da hukuncin da aka yi wa wani Danꞌuwa mai suna Boris Simonenko. Alkalin bai fadi irin hukunci da za a yanke wa Danꞌuwa Simonenko ba.
Tarihinsa
Muna da tabbaci cewa Boris da iyalinsa za su ci gaba da samun karfi da farin ciki yayin da suke kusa da Jehobah.—1 Tarihi 16:27.
Lokaci
8 ga Fabrairu, 2021
Hukuma ta dauka muryar Danꞌuwa Boris yayin da yake waya domin su yi amfani da shi wajen yin bincike
17 ga Fabrairu, 2021
An yi bincike a gidansa. An yi masa tambayoyi kuma aka kulle shi na dan lokaci
18 ga Fabrairu, 2021
An soma tuhumarsa da aikata laifi. Laifinsa shi ne yana gudanar da taron Shaidun Jehobah ta intane. An tsare shi kafin a yanke masa hukunci
13 ga Yuli, 2021
An sake shi kuma aka tsare shi a cikin gidansa
17 ga Fabrairu, 2022
An sake shi amma an hana shi barin kasar
15 ga Satumba, 2022
An soma yi masa shariꞌa a kotu