Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Vladimir Alushkin da matarsa, Tatyana

16 GA SATUMBA, 2020
RASHA

Dan’uwa Vladimir Alushkin Ba Zai Koma Kurkuku Ba

Dan’uwa Vladimir Alushkin Ba Zai Koma Kurkuku Ba

A ranar 16 ga Satumba, 2020, Kotun Yankin Penza ta sanar da hukuncin da ta yanke a kan karar da aka daukaka da ta shafi Dan’uwa Vladimir Alushkin da Vladimir Kulyasov, da Andrey Magliv, da Denis Timoshin, da kuma ’Yar’uwa Tatyana Alushkina da Galiya Olkhova. Kotun ta ce a maimakon Dan’uwa Alushkin ya yi shekara shida a kurkuku, zai yi shekara hudu ana sa masa ido kuma za a ba shi wasu dokoki, amma ba za a kai shi kurkuku ba. Muna farin ciki cewa ba za a komar da shi kurkuku ba. Ba a canja hukuncin da aka yanke wa sauran ’yan’uwan cewa ba za a kai su kurkuku ba.