Koma ka ga abin da ke ciki

Daga hagu zuwa dama: Dan’uwa Vladimir Khokhlov da ’Yar’uwa Tatyana Shamsheva da ’Yar’uwa Olga Silaeva, da Dan’uwa Eduard Zhinzhikov

3 GA SATUMBA, 2020
RASHA

Kotu Ta Kama ’Yan’uwa Maza Biyu da Mata Biyu da Laifi Saboda Imaninsu

Kotu Ta Kama ’Yan’uwa Maza Biyu da Mata Biyu da Laifi Saboda Imaninsu

Hukuncin

A ranar 3 ga Satumba, 2020, Kotun Garin Novozybkov a Yankin Bryansk ya kama Dan’uwa Vladimir Khokhlov, da ’Yar’uwa Tatyana Shamsheva da ’Yar’uwa Olga Silaeva, da kuma Dan’uwa Eduard Zhinzhikov da laifi. An yanke musu hukuncin dauri na tsawon shekara daya zuwa shekara daya da wata uku. Amma ba za a kai su kurkuku ba da yake an riga an daure su a kurkuku na tsawon lokacin nan kafin a yanke musu hukunci.

Karin Bayani

Vladimir Khokhlov

  • Shekarar Haihuwa: 1977 (Garin Novozybkov, a Yankin Bryansk)

  • Tarihi: Shi makaniki ne kuma ya yi aikin soja kafin ya zama Mashaidin Jehobah. Yana son buga kwallon kafa da karatu da kamun kifi da kuma kada jita.

  • Wani abokinsa ne ya ba shi shawara ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya auri Olga a 2007 kuma sun haifi ’ya mai suna Anastasia. Dukansu suna bauta wa Jehobah

Tatyana Shamsheva

  • Shekarar Haihuwa: 1977 (Birnin Cherepovets, a Yankin Vologda)

  • Tarihi: Ita masanar tattalin arziki ce kuma ta dade tana koyar da ilimin tattalin arziki da ilimin lauyoyi da ilimin akanta a makaranta. Ta yi baftisma a 1995. Tana jin dadin koya wa mutane ka’idodi masu kyau da ke Littafi Mai Tsarki

Olga Silaeva

  • Shekarar Haihuwa: 1988 (Kauyen Davydovo a Yankin Moscow)

  • Tarihi: Ita ce ’yar auta a cikin yara uku. Ta je makarantar fasaha inda ta sami difuloma. Tana son yin kayan ado da allura da zare, da karatu da kuma buga kwallon raga ta Volley. Misalin mahaifiyarta ne ya sa ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta soma rayuwar da ta jitu da koyarwarsa

Eduard Zhinzhikov

  • Shekarar Haihuwa: 1971 (Garin Novozybkov a Yankin Bryansk)

  • Tarihi: Ya taba aikin welda da aikin shara kuma ya taba aiki da ’yan sanda. A dā yana wata kungiyar mawaka. Daga baya ya auri wata ’yar kungiyar mai suna Tatyana, a 1993. Yana son rubuta wakoki da kuma kada jita

  • Dab da shekara ta 2000 ne ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma hakan ya sa ya sami amsoshin tambayoyinsa game da rayuwa. Hakan ya sa shi ya canja halinsa kuma ya inganta zaman iyalinsa. Yadda ya gyara rayuwarsa ya burge matarsa kuma daga baya ita ma ta zama Mashaidiyar Jehobah

Yadda Labarin Ya Soma

A ranar 11 ga Yuni, 2019, hukumomin kasar Rasha sun kai sumame a gidajen Shaidun Jehobah guda 22 da ke Yankin Bryansk a Rasha. A lokacin ne aka kama ’Yar’uwa Tatyana Shamsheva da ’Yar’uwa Olga Silaeva kuma sun yi kwana 245 a kulle. An sake su a Mayu 2020 kuma sun koma gida suna jiran hukuncin da za a yanke a kansu.

A ranar 16 ga Oktoba, 2019, hukumomin sun shigar da karar Dan’uwa Vladimir Khokhlov da Dan’uwa Eduard Zhinzhikov a kotu. Daga baya an hada karar da na ’Yar’uwa Shamsheva da ’Yar’uwa Silaeva. Bayan kwana bakwai an kama ’yan’uwa mazan an kulle su ba tare da an yi musu shari’a ba.

A hira da aka yi da ’yan’uwa mata biyun nan a 2020 Karin Bayani na 5 Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, ’Yar’uwa Silaeva ta ce watanni takwas da ta yi a kulle ya kara tabbatar mata cewa “ko da yanayinmu ya yi muni sosai, Jehobah zai ci gaba da ba mu ruhunsa mai tsarki don ya taimaka mana mu jimre.” ’Yar’uwa Shamsheva kuma ta ce: “Jehobah yana tare da mu a kullum, yana karfafa mu kuma yana taimaka mana.”

Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da taimaka wa ’yan’uwanmu a Rasha da ake kokarin jefa su a kurkuku da wadanda suke kurkuku. Zai ba su kwanciyar hankali don su ci gaba da yin farin ciki yayin da suke jimre tsanantawar.​—1 Korintiyawa 10:13.