Koma ka ga abin da ke ciki

27 GA JANAIRU, 2020
RASHA

Kotun Rasha ta Yanke Hukunci A Kan Dan’uwa Aleksandr Prianikov da ʼYar’uwa Venera da Darya Dulova

Kotun Rasha ta Yanke Hukunci A Kan Dan’uwa Aleksandr Prianikov da ʼYar’uwa Venera da Darya Dulova

A ranar 27 ga Janairu, 2020, kotun Karpinsk City Court ta tsare Dan’uwa Aleksandr Prianikov, tare da ʼYar’uwa Venera da Darya Dulova. Kotun ta yanke musu hukuncin shekara biyu da rabi da shekara biyu da kuma shekara daya. Ko da yake ba za a saka su a kurkuku a wannan lokacin ba, za a rika saka musu ido a wadannan shekarun da ya kamata su yi a kurkuku. Za su daukaka kara.