17 GA DISAMBA, 2019
RASHA
Kotun Rasha ta Yanke wa Dan’uwa Alushkin Hukuncin Yin Shekaru 6 A Kurkuku, ’Yan’uwa Biyar Kuma Za a Rika Saka Musu Ido
A ranar Jumma’a da safe, 13 ga Disamba, 2019, kotun da ke yankin Leninsky Penza ta yanke wa Dan’uwa Vladimir Alushkin hukuncin yin shekara shida a kurkuku. Nan da nan aka saka masa ankwa aka tafi da shi. Kari ga haka, ana tuhumar ’yan’uwa biyar har da matar Vladimir mai suna Tatyana. Kotu ta yanke hukunci cewa ’yan’uwan biyar din (maza uku da mata biyu) ba za su je kurkuku ba, amma za a rika saka musu ido, idan suka taka doka za a saka kowannensu a kurkuku na shekara biyu. Duka ’yan’uwa shida za su daukaka kara.
Kamar yadda aka ambata dazu, an kama Dan’uwa Vladimir Alushkin, a ranar 15 ga Yuli, 2018, bayan ’yan sanda 12 rike bindigogi da suka rufe fuskokinsu suka shiga gidansa. Sun dau tsawon awa hudu suna bincike a gidan dan’uwan kuma suka kwashe wayoyi da telibijin da Littafi Mai Tsarki da wasu littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. ’Yan sanda sun kuma bincika gidajen ’yan’uwa biyar a ranar, kuma suka kama ’yan’uwa kusan 40 don su yi musu tambayoyi.
Hukumar sun tsare dan’uwa Alushkin a kurkuku na kwana biyu kafin Kotun Pervomayskiy District Court ta ba da umurnin canja wurin da za a tsare dan’uwan na tsawon wata biyu kafin a yanke masa hukunci. Bayan wannan, kotun ta dada tsawon kwanaki da dan’uwa Vladimir Alushkin zai yi a bayan kanta kafin a yi shari’a. Bayan kusan wata shida a bayan kanta, sai aka kai Dan’uwa Alushkin gida don a tsare shi, kafin aka yanke masa hukunci a ranar 13 ga Disamba.
’Yan’uwa uku daga biyar da aka tsare su da dan’uwa Alushkin su ne dan’uwa Vladimir Kulyasov da Andrey Magliv da Denis Timoshin. An tsare su a gida har sai lokacin da aka kammala bincike da shari’ar. Sauran ’yan’uwa biyun mata ne masu suna Tatyana Alushkin da Galiya Olkhova. Tun watan Fabrairu 2019, hukuma ta saka musu takunkumin hana tattauna wa da mutane da kuma yin tafiya.
A watan Agusta 2019, Kungiyar da ake kira Working Group on Arbitrary Detention na Majalisar Dinkin Duniya ta rubuta rahoto shafi 12 don ta bayyana cewa tsare Alushkin da Rasha ta yi bai dace ba. Kungiyar ta ce bai kamata a kama dan’uwa Alushkin ko a tsare shi ba tare da an yi masa shari’a ba. Kungiyar ta ce abin da ya kamata Rasha ta yi shi ne ta saki Dan’uwa Alushkin. Da suke kāre ’yancin ’yan’uwa shida da aka tsare a birnin Penza, lauyoyin sun yi la’akari ne da ra’ayin kungiyar game da wadanda aka tsare a kurkuku ba tare da hujja ba. Duk da haka, a lokacin da alkalin yake karanta hukuncin da aka yanke a ranar 13 ga Disamba, ya ce ya bi hukuncin da Kotun Koli a Rasha ta yanke a shekara ta 2017 cewa an haramta duk ayyukan Shaidun Jehobah, kuma ya ce wannan hukunci ne ya fi na kungiyar Working Group on Arbitrary Detention na Majalisar Dinkin Duniya.
A shekarar nan, Rasha ta tsare ’yan’uwa 18. An yanke wa ’yan’uwa 9 daga cikinsu hukuncin zuwa kurkuku. Fiye da ’yan’uwa 40 ne suke bayan kanta suna jiran shari’a, an tsare ’yan’uwa 19 kuma a gida. A kasar Rasha gabaki daya, kusan ’yan’uwan 300 ne suke fuskantar zargin laifuffuka game da ibadarsu.
Ko da yake muna bakin ciki cewa ana tsananta wa ’yan’uwan, ba ma mamaki abubuwan nan suna faruwa. An annabta cewa wadannan abubuwan za su rika faruwa kuma Jehobah zai taimaka mana. Muna addu’a don “ruhu mai daukaka, wato Ruhun Allah” ya kasance tare da su.—1 Bitrus 4:12-14.