Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Yegor Baranov da ’Yar’uwa Darya Dulova

8 GA SATUMBA, 2020
RASHA

Matasa Biyu da Suke Nuna Bangaskiya da Karfin Zuciya

Matasa Biyu da Suke Nuna Bangaskiya da Karfin Zuciya

’Yan’uwanmu matasa biyu a Rasha, wato Dan’uwa Yegor Baranov da ’Yar’uwa Darya Dulova suna nuna karfin zuciya duk da cewa za a iya kama su da laifi kuma a tsare su a kurkuku na lokaci mai tsawo sosai. A yanzu haka an tsare su ba tare da an yi musu hukunci ba, kuma Dan’uwa Baranov shekarunsa 19 ne kawai. ’Yar’uwa Dulova kuma shekarunta 18 ne kacal a lokacin da hukumomi a Rasha suka kai sumame a gidansu. Su ne mafi karancin shekaru a cikin ’yan’uwa maza da mata guda 380 da ake zarginsu da laifi don imaninsu a Rasha.

Tun ran 27 ga Mayu, 2020 ne aka tsare Dan’uwa Baranov. ’Yar’uwa Dulova kuma, kararraki biyu ne aka shigar a kanta. Tana jiran hukuncin da za a yanke a kanta. Duk da yanayin da suke ciki, su biyun sun kudura cewa za su rike amincinsu ga Jehobah.

A ranar 27 ga Mayu, jami’an tsaron da ake kira Federal Security Service (FSB) dauke da makamai, sun kai sumame a gidan da Dan’uwa Baranov yake zama da mahaifiyarsa. Daga baya, Alkali Aleksey Shatilov ya ba da umurni a tsare dan’uwan kafin a yi masa hukunci domin a cewarsa, shi “daya daga cikin shugabannin” Shaidun Jehobah ne a yankin.

Yadda jami’an tsaron suka shiga gidansu abin ban tsoro ne, amma Dan’uwa Baranov ya ce abin da ya taimaka masa ya natsu shi ne, ya yi addu’a ga Jehobah. Ya kuma ce: “Daya daga cikin jami’an tsaron da suka binciki gidanmu ya ce na yi kamar da ma ina jiransu ne.”

Dan’uwa Baranov ya ce ya dinga gaya wa kansa cewa, “da yake Jehobah ya kyale hakan ya faru, to lalle zan iya jimrewa.” Ya dada da cewa: “Yin addu’a da dukan zuciyata, ina rokon Jehobah ya taimaka min kuma ya ba ni ruhunsa mai tsarki, ya sa ban ji tsoro ba. Ban da haka, na san cewa ban yi wani laifi ba. Zuciyata ba ta damu na, ana tsananta min ne domin imanina.”

Dan’uwa Baranov ya bayyana cewa ba ya jin tsoro a kurkukun. Wadanda suke kurkukun ba sa wulakanta shi, maimakon haka, suna daraja shi kuma suna daukansa kamar kaninsu. Dan’uwa Baranov ya ce: “Sun san cewa bai kamata a tsare ni ba.”

A ranar 1 ga Agusta, 2018, jami’an tsaro sun shiga gidan da ’Yar’uwa Dulova take zama da mahaifiyarta. ’Yar’uwa Dulova ta ce yadda aka shiga kuma aka bincika gidansu ya daga mata hankali, amma duk da haka, bangaskiyarta na nan daram. Ta ce: “Na riga na kudura cewa zan rike amincina ga Jehobah, zan bauta masa har karshe ko da me zai faru.”

A watan Satumba 2019 ne aka soma saurarar karar da aka shigar a kan ’Yar’uwa Dulova a Kotun Birnin Karpinsky da ke Yankin Sverdlovsk. A daya daga cikin lokuta na karshe da aka saurari karar, ’Yar’uwa Dulova ta gaya wa kotun cewa mutane sukan so su gaya wa abokansu abubuwan da ke sa su farin ciki. Ta bayyana cewa: “Alal misali, na san cewa nan ba da dadewa ba, Allah zai mai da duniyar nan aljanna, wurin da mutane ba za su kara yin bakin ciki ba. Wannan ba abu mai kyau da ya kamata in gaya wa makwabtana ba ne?”

Duk da wannan bayani mai gamsarwa da ta bayar, an kama ta da laifi a ranar 27 ga Janairu, 2020. An yanke wa ’Yar’uwa Dulova hukuncin yin shekara daya ana sa mata ido kuma an kafa mata wasu dokoki. Lauyan da ke tsaya mata ya daukaka kara.

A ranar 6 ga Agusta, 2020, Kotun Yankin Sverdlovsk ya ce bai kamata a kama ’Yar’uwa Dulova da laifi ba. Sai aka mai da karar zuwa Kotun Birnin Karpinsky kuma aka ce wani alkali ya sake duba karar. Ba a saka ranar da za a sake sauraron karar ba tukun. Yayin da take jiran hukuncin da za a yanke, tana iya kokarinta tare da mahaifiyarta da wasu Shaidu uku don su nuna cewa ba su da laifi a wata kara dabam da ake sauraro.

Dan’uwa Baranov da ’Yar’uwa Dulova sun koyi darussa sosai daga tsanantawar da ake musu.

’Yar’uwa Dulova ta fadi abin da ya taimaka mata, ta ce: “Ka karfafa dangantakarka da Jehobah ta wajen karanta Kalmarsa da yin shiri don taronmu da kuma koyan wakokinmu. Ka yi ta tunani a kan nassosin da za su taimaka maka ka daina damuwa da kuma jin tsoron abin da zai iya faruwa da kai a nan gaba.”

Dan’uwa Baranov ya ce: “Idan kana so ka jimre tsanantawa, wajibi ne ka kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Kar ka bata lokaci, ka karfafa dangantakarka da Jehobah yanzu.”

Akwai labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah ya taimaka wa matasa masu aminci, su kasance da karfin zuciya. Mun san zai ci gaba da taimaka wa ’yan’uwanmu matasa da ake tsananta musu a Rasha da sauran wurare a duniya.​—1 Sama’ila 1:20; 16:18; 2 Sarakuna 5:​1-3; Daniyel 1:​14-17; 3:​17-27.