21 GA SATUMBA, 2020
RASHA
Rasha Tana Yunkurin Kama Dan’uwa Konstantin Bazhenov, da Matarsa da Wata ’Yar’uwa Mai Shekara 73 da Laifi
Ranar da Za A Yanke Hukuncin
A ranar 25 ga Satumba, 2020, * Kotun Gundumar Yelizovsky da ke Yankin Kamchatka zai sanar da hukuncinsa a kan karar da aka shigar da ta shafi Dan’uwa Konstantin Bazhenov, da matarsa, Snezhana, da ’Yar’uwa Vera Zolotova. Wanda ya shigar da karar yana so a ci wa Dan’uwa Bazhenov da matarsa tarar dala 7,850 (wajen naira 2,990,850) kuma a ci wa ’Yar’uwa Zolotova tarar dala 5,235 (wajen naira 1,997,152).
Karin Bayani
Konstantin Bazhenov
Shekarar Haihuwa: 1977 (Petropavlovsk-Kamchatsky, a Yankin Kamchatka)
Tarihi: Shi ne dan fari a cikin yara hudu. Shi makaniki ne a dā kuma ya yi koyarwa a wata makarantar fasaha. Yana jin dadin kamun kifi
Ya auri Snezhana a shekara ta 2001, ita ma malama ce. Suna da ’ya mai suna Elizabeth, kuma dukansu suna bauta wa Jehobah
Snezhana Bazhenova
Shekarar Haihuwa: 1977 (Shikotan Island, Sakhalin Oblast)
Tarihi: Mamarta ce kadai ta yi renon ta. Tana kaunar yara sosai kuma tana jin dadin koyar da yaran da suke firamare. Yanzu an hana ta yin aikin da zai hada ta da kananan yara domin ana zarginta da aikata laifi
Kakarta ce ta koya mata game da Allah da yadda za ta rika yin addu’a. Hakan ya taimaka mata ta kaunaci Allah da kuma Littafi Mai Tsarki
Vera Zolotova
Shekarar Haihuwa: 1946 (Yelizovo, a Yankin Kamchatka)
Tarihi: Ta taso ne a iyali mai yara da yawa. Kuma ta auri Yuri Zolotov a shekara ta 1966. Sun haifi yara biyu. Ta yi aikin akanta amma yanzu ta yi ritaya. Tana son hawan tuddai da yin wasan kankara da kuma gudu a kan kankara
Ta yi shekaru da dama tana kokari ta san Allah, kuma ta bincika addinai da dama. Daga baya, ta yi murna sosai da ta koya cewa Allah mai adalci ne kuma yana kaunar mutane. Har wa yau, maigidanta ba Mashaidin Jehobah ba ne. Duk da haka, yadda Littafi Mai Tsarki ya sa ta gyara halinta ya burge shi
Yadda Labarin Ya Soma
A ranar 19 ga Agusta, 2018, ’yan sanda sun bincika gidajen Shaidun Jehobah guda uku a garin Yelizovo, kuma sun kama ’yan’uwa maza da mata guda 11. An yi awoyi da dama ana musu tambayoyi. Daga baya an saki guda takwas daga cikinsu. Sa’an nan suka shigar da karar Dan’uwa Bazhenov da matarsa, da ’Yar’uwa Zolotova. An tsare su a wani wuri da ake tsare mutane na dan lokaci. Bayan kwana biyu, an saki ’yan’uwa matan, amma wani alkali ya ba da umurni cewa a ci gaba da tsare Dan’uwa Bazhenov. Bayan kwana takwas, shi ma aka sake shi.
Muna addu’a Jehobah ya taimaka wa Dan’uwa Bazhenov da matarsa, da ’Yar’uwa Zolotova su ci gaba da dogara gare shi yayin da suke jiran shari’ar da za a yi a kansu. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci cewa Jehobah zai sa bayinsa su sami farin ciki da kwanciyar hankali, kuma za su “yalwata da sa zuciya ta wurin ikon ruhu mai tsarki.”—Romawa 15:13.
^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar