Koma ka ga abin da ke ciki

24 GA NUWAMBA, 2020
RASHA

Wani Kotu a Rasha Ya Yanke wa Dan’uwa Sergey Ledenyov Hukuncin Yin Shekara Biyu Yana Bin Wasu Dokoki da Za A Ba Shi

Wani Kotu a Rasha Ya Yanke wa Dan’uwa Sergey Ledenyov Hukuncin Yin Shekara Biyu Yana Bin Wasu Dokoki da Za A Ba Shi

A ranar 24 ga Nuwamba, 2020, Kotun Birnin Petropavlovsk-Kamchatskiy da ke Yankin Kamchatka ya kama Dan’uwa Sergey Ledenyov da laifi. Kotun ya ce zai yi shekara biyu yana bin wasu dokoki da za a ba shi, kuma za a yi shekara uku ana sa masa ido. A yanzu ba za a kai shi kurkuku ba.

A rana ta karshe da aka saurari karar, Sergey ya yi karfin hali kuma ya bayyana abin da ake nufi mutum ya zama Mashaidin Jehobah. Ya ce: Jehobah ba sunan wasu mutane, ko kungiya, ko addini ba ne. Jehobah sunan Allah ne da kansa. A littafin annabi Ishaya, Jehobah ya kira amintattun bayinsa ’shaiduna.’ Shi ya sa muka soma amsa sunan nan ’Shaidun Jehobah’ a wani babban taro da aka yi a 1931. Wannan sunan ya nuna aikin da Allah ya ba mu mu zama shaidunsa, wato mu sanar wa mutane cewa shi ne Mahalicci, da Mai Ceto, da Mafi Iko a sama da kasa, kuma mu sanar wa mutane abin da yake shirin yi wa ’yan Adam a nan gaba. Babban gata ne Allah ya ba ni da suaran ’yan’uwana masu bi.”​—Ishaya 43:10.

Da gaba gadi, Sergey ya gaya wa kotun cewa: Ba ni da wani dalilin jin kunya, domin ban aikata wani laifi ba. Zuciyata ba ta damu na don ban da laifi a gaban Allah da kuma ’yan Adam.”