Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Sergey Rayman da matarsa, Valeriya

7 GA SATUMBA, 2020
RASHA

Wani Kotu a Rasha Yana So Ya Hukunta Wasu Ma’aurata

Wani Kotu a Rasha Yana So Ya Hukunta Wasu Ma’aurata

Ranar da Za A Yanke Hukuncin

A ranar 16 ga Satumba, 2020, * Kotun Gunduma na Sverdlovskiy a birnin Kostroma zai sanar da shari’ar da ya yanke a kan Dan’uwa Sergey Rayman da matarsa, Valeriya. Za a iya yanke musu hukuncin dauri na tsawon shekara bakwai amma ba za a kai su kurkuku ba.

Karin Bayani

Sergey Rayman

  • Shekarar Haihuwa: 1996 (Garin Kineshma, a Yankin Ivanovo)

  • Tarihi: Ya yi karatu a kan yin gine-gine a wata makarantar fasaha kuma ya zama kwararre a fannin tsara yadda cikin gida zai kasance, (interior design). Kakarsa ce ta koya masa game da Littafi Mai Tsarki. Ya auri Valeriya a shekara ta 2015. Yana son dahuwa da yin tsere kan dusar kankara.

Valeriya Rayman

  • Shekarar haihuwa: 1993 (Garin Sharya, a Yankin Kostroma)

  • Tarihi: Mahaifinta ya rasu sa’ad da take ’yar shekara goma. Mahaifiyarta ce ta koya mata game da Jehobah. ’Yar’uwa Rayman ta kware wajen gyaran gashi.

Yadda Labarin Ya Soma

Da sassafe a ranar 25 ga Yuli, 2018, ’yan sanda rike da bindigogi sun yi amfani da wani karfe wajen balle kofar gidan Dan’uwa Rayman da matarsa. Bayan haka, sai suka shiga gidan kuma suka kama su. ’Yar’uwa Rayman ta yi kwanaki biyu a tsare. Dan’uwa Rayman kuma an rufe shi a inda ba zai iya yin ma’amala da kowa ba na tsawon kwanaki 59. Hukumar kasar ta takaita sha’ani da za su iya yi da sauran Shaidun Jehobah. Kari ga haka, an hana su fita daga gida da yamma. Wannan yanayin ya sa su cikin tsaka mai wuya sosai.

Yayin da ma’auratan nan suke jiran shari’ar da kotu zai yanke, muna rokon Jehobah ya taimaka musu su ci gaba da kasancewa da karfin zuciya da kuma tabbaci cewa ba zai taba barinsu ba.​—Yoshuwa 1:9.

^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar